PDP vs APC: Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari’ar Gwamnan Jihar Sokoto

PDP vs APC: Kotun Koli Ta Yanke Hukuncin Karshe Kan Shari’ar Gwamnan Jihar Sokoto

  • Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan zaben gwamnan jihar Sokoto, inda ta ayyana Ahmad Aliyu matsayin wanda ya lashe zaben
  • Jam'iyyar PDP da dan takararta Sa'idu Umar ne suka shigar da karar, tare da rokon kotun ta ayyana Umar wanda ya lashe zaben
  • Sai dai kotun a hukuncin da ta yanke, ta ce PDP ta gaza gabatar da wasu kwararan hujjoji da za su tabbatar da cewa an tafka magudi a zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Yanzu ne muka samu labarin cewa Kotun Koli ta ayyana Ahmad Aliyu na jam'iyyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar Taraba.

Hakan na nufin Kotun Kolin ta yi watsi da korafe-korafen da dan takarar PDP, Sa'idu Umar ya yi saboda karancin kwararan hujjoji, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan takaddamar zaben gwamnan PDP, ta fadi dalili

Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari’ar gwamnan jihar Sokoto
PDP vs APC: Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe kan shari’ar gwamnan jihar Sokoto. Hoto: Ahmad Aliyu
Asali: Twitter

Mai shari’a Tijani Abubakar ya sanar da hukuncin kotun da ke karkashin jagorancin mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP da Farfesa Yahaya sun kalubalanci zaben Ahmed Aliyu

Wanda ya shigar da kara ya kalubalanci zaben Aliyu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben watan Maris na 2023.

Umar da PDP sun bukaci kotun koli ta yi watsi da hukunce-hukuncen kotunan daukaka kara da na kotun zaben jihar.

Ya bayyyana cewa an tafka kura-kuran zabe, rashin bin dokar zabe a matsayin dalilan da suke so a soke zaben Aliyu.

Hukuncin da Kotun Daukaka Kara da kotun zabe suka yanke

Ya roki kotun da ta bayyana shi a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben, ko kuma a madadinsa ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba tare da ba da umarnin sake zabe a rumfunan zabe kusan 138.

Kara karanta wannan

NNPP Vs Kefas: Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnan jihar Taraba

A shekarar da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Aliyu na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga Maris.

Aliyu ya samu kuri’u 453,661 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Umar wanda ya samu kuri’u 404,632.

Kotu ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Taraba

A wani labarin makamancin wannan, Kotun Koli ta ce Agbu Kefas, shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Taraba, kamar yadda hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ayyana a watan Maris, 2023.

Jam'iyyar NNPP da dan takararta, Farfesa Yahaya Sani ne suka shigar da kara gaban kotun, inda suka kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun zaben jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel