“Ta Karewa Ganduje”: Jigon PDP Ya Yi Hasashen Mataki Na Gaba da Gwamnan Kano Zai Dauka Bayan Nasara

“Ta Karewa Ganduje”: Jigon PDP Ya Yi Hasashen Mataki Na Gaba da Gwamnan Kano Zai Dauka Bayan Nasara

  • Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, mamba a jam'iyyar PDP, ya yi hasashen cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ubangidansa, Rabiu Kwankwaso, za su sauya sheka zuwa APC
  • Abubakar ya yi wannan hasashen ne bayan hukuncin Kotun Koli da ta mayar da Gwamna Yusug kan kujerarsa tare da soke hukuncin tsige shi
  • Jigon na PDP ya yarda cewa wannan yunkurin zai yi illa ga siyasar shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda ya gaza samawa dan takararsa a zaben na 2023 nasara

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar, wani mamba a jam'iyyar PDP, ya yi hasashen cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ubangidansa a siyasa, Rabiu Kwankwaso, za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida-Gida ya aika muhimmin sako ga Gawuna bayan hukuncin Kotun Koli

Abubakar, darakta janar na kungiyar Atiku, ya wallafa hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, bayan Kotun Koli ta soke hukuncin da ya tsige Gwamna Yusuf daga kujerarsa.

Jigon PDP ya yi hasashen sauya shekar Abba da Kwankwaso zuwa APC
“Ta Karewa Ganduje”: Jigon PDP Ya Yi Hasashen Mataki Na Gaba da Gwamnan Kano Zai Dauka Bayan Nasara Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jigon na PDP ya kuma ce hasashen komawar Gwamna Yusuf da Kwankwaso APC zai lalata siyadar shugaban jam'iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya rubuta:

"Ta karewa Ganduje! Ina da tabbaccin cewa Abba da Kwankwaso za su koma APC yanzu ko a nan gaba."

Ganduje ya yi aiki tukuru gabannin zaben 2023 don tabbatar da ganin dan takarar da yake so, Nasir Yusuf Gawuna, ya gaje shi.

Sai dai kuma, Gwamna Yusuf na jam'iyyar NNPP ya kayar da shi a zaben. Kokarinsa na ganin sun kwato kujerar gwamnan Kano ya tashi tutar babu yayin da Kotun Koli ta yanke hukunci a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli kan zaben Kano: Kwankwaso ya magantu, ya aika sako ga yan Najeriya

Jama'a sun yi martani kan hasashen Abubakar

A halin da ake ciki, martanin jama'a kan hasashen Abubakar a dandalin X ya nuna cewa mutane da dama basu yarda da wannan batu nasa ba.

Diamond, @DareHardy09, ya ce:

"Wato kana tsammanin Tinubu zai sadaukar da Ganduje kan Kwankwaso?? A'a ba zai faru ba."

Captain Tango, @Capolutiti, y fada ma jigon na PDP:

"A kullun hasashenka cike yake da tangarda."

AMANOZEE, @AlasahMomoh, ya ce:

"Idan har Ganduje ne shugaban APC na kasa, Abba ba zai sauya sheka."

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba

A baya Legit Hausa ta kawo cewa Kotun Kolin Najeriya ta da Abba Kabir Yusuf kan kujerarsa na gwamnan jihar Kano, a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu.

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanto hukuncin ya bayyana cewa kotun kasar ta yi kuskure a hukuncinta na rage kuri'u 165,616 daga adadin kuri'un da gwamnan ya samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel