Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano

  • Bayan shafe tsawon watanni ana fafatawa a kotuna daban-daban, daga karshe Kotun Koli ta raba gardama a takaddamar zaben gwamnan jihar Kano
  • A ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu ne babbar kotun kasar ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan na 18 ga watan Maris 2023
  • Alkalan kotun sun yi fatali da hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Gwamna Yusuf daga kujerarasa tare da ayyana dan takarar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya ci zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da zaben Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano, a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairu, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan na Kano, Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar gwamnan PDP a Arewa, ta fadi dalili

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanto hukuncin ya bayyana cewa kotun kasar ta yi kuskure a hukuncinta na rage kuri'u 165,616 daga adadin kuri'un da gwamnan ya samu.

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a zaben gwamnan jihar Kano
Kotun Koli Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kotun Kolin ta kuma riki cewa alkalai ba su da ikon amfani da dokar zabe wajen rusa kuri’un da aka kada da sunan jam’iyyar NNPP a zaben na ranar 18 ga watan Maris din 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da suke watsi da karar da APC ta shigar, kwamitin kotun sun nuna gamsuwa cewa babu abin da ke nuna ba daga wajen hukumar INEC kuri’un su ka fito ba.

Da take zartar da hukunci kan haka, kotun ta ce kuri’a ba ta haramta saboda rashin sa hannu da tambarin INEC.

Menene matsayin Kotu kan cewa Abba ba dan jam'iyya bane?

Kan batun cewa Abba ba dan jam'iyyar NNPP bane, Okoro ya bayyana cewa babu ruwan kotu a wannan lokaci da gardamar zama dan jam’iyya, ya ce wannan hurumin ‘ya ‘yan jam’iyya ne ba na kotun ba.

Kara karanta wannan

Dauda Vs Matawalle: Kotun ƙoli ta bayyana sahihin wanda ya ci zaben gwamna a jihar Zamfara

Da wannan hukunci na babbar kotun kasar, jam'iyyar NNPP ta tabbata a matsayin mai mulki a jihar Kano, Daily Trust ta rahoto.

Tun farko dai hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Abba a matsayin zababben gwamnan jihar amma sai jam'iyyar APC ta kalubalanci nasararsa a kotu.

Legit Hausa ta tuntubi wasu Kanawa don jin yadda suka samu hukuncin Kotun Koli da ta tabbatar da Abba.

Zainab Ummi ta ce:

“Yau kowa ya san mu Kanawa muna cikin farin ciki. Tabbass na kara yarda addu’ar mumini bata faduwa kasa banza.
“A daidai lokacin da muka yanke kauna da cewa Abbanmu zai yi nasara sai Allah buwayi ya yi ikonsa.
“Muna rokon Allah ya sa wannan zabi da ya yi mana ya zamo mafi alkhairi a garemu gaba daya.”

Hajiya Tabawa Inuwa kuwa cewa ta yi:

“Alhamdulillahi muna godiya ga Allah bisa wannan hukunci da ya yi. Lallai muna farin ciki da nasarar da Abba ya samu a Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya maida martani bayan kotun ƙoli ta yanke hukunci, ya gode wa wanda ya ba shi nasara

“Dama shine ya ci zabe aka so yi masa fin karfi amma Allah bai nufa ba. Allah ya sa ya zamo mana alkhairi da kasa baki daya.”

Gwamnan Bauchi ya yi nasara a Kotun Koli

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa Kotun Koli ta tabbatar da nasarar zaben Bala Mohammed matsayin gwamnan jihar Bauchi.

Kotun ta yi watsi da ƙarar da APC da dan takararta Sadique Abubakar suka shigar na kalubalantar hukuncin Kotun Daukaka Kara da na kotun sauraron kararrakin zaben jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: