Bidiyon Mahaifiyar Abba Ta Hadu Da Maman Sanusi, An Yi Batun Dawo da Sarki Sarautar Kano

Bidiyon Mahaifiyar Abba Ta Hadu Da Maman Sanusi, An Yi Batun Dawo da Sarki Sarautar Kano

  • Maman Abba Kabir Yusuf tayi zama da mahaifiyar Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II
  • Ana tunanin Hajiya Saudatu Hussain ta hadu da Khadijatul-Naja'atu ne bayan hukuncin kotun koli
  • Tsofaffin sun yi wa jihar Kano addu’o’i, aka kuma roki Allah SWT ya maida Khalifa cikin gidan dabo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Mahaifiyar Mai girma Abba Kabir Yusuf ta kai ziyara wajen tsohuwar Mai martaba Muhammadu Sanusi II.

Wani bidiyo da Legit ta samu a dandalin sada zumunta ya nuna Khadijatul-Naja'atu Yusuf tare da mahafiyar Khalifa.

Sanusi II Abba
Muhammadu Sanusi II, Sarki da Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf, Kabir Dakata
Asali: Facebook

Haduwar iyayen masu mulkin Kano

Hajiya Khadijatul-Naja'atu Yusuf ta ziyarci Hajiya Saudatu Hussain ne jim kadan bayan an ji hukuncin kotun koli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Alkalan kotun koli sun tabbatar da Abba Kabir Yusuf ne zababben gwamnan Kano bayan watannin shari’a da APC.

Kamar yadda aka ji a bidiyon da hadimin gwamna, Abdullahi Ibrahim ya wallafa, tsofaffin sun yi wa Kano addu’o’i.

An yi wa Muhammadu Sanusi II addu'a

Wadannan Bayin Allah sun yi wa gwamna Abba Kabir Yusuf addu’ar samun nasara wajen jagorantar al’ummar Kano.

Maman gwamnan ta nuna akwai bukatar Sanusi II ya koma gidan sarauta domin cigaba da alherin da ya yi niyya.

Gidan Sanusi II a sarautar Kano

Saudatu Hussain ce mahaifiyar Sarkin Kano na 14 watau Muhammadu Sanusi II wanda aka cire daga mulki a 2019.

Mai gidanta Aminu Sanusi ya rike sarautar Ciroman Kano kafin rasuwarsa, yana cikin ‘ya ‘yan Muhammadu Sanusi I.

Shi kuwa Sanusi I shi ne babban yaron Sarkin Kano Abdullahi Bayero da ya rasu a 1953.

Hadimin gwamna ya ce an yi haka

Kara karanta wannan

"Ta karewa Ganduje": Jigon PDP ya yi hasashen mataki na gaba da gwamnan Kano zai dauka bayan nasara

Legit ta tuntubi Abdullahi Ibrahim, ya kuma tabbatar mata da cewa mahaifan jagororin na Kano sun hadu a jiya.

Abdullahi Ibrahim ya ce a ranar Juma’a ne maman mai gidansu watau gwamna ta ziyarci mahaifiyar Mai martaban.

Ana ta rade-radin gwamnatin Kwankwasiyya ta NNPP za tayi kokarin dawo da Muhammadu Sanusi II mulki.

Tun da za a rantsar da Abba, ya gayyaci Muhammadu Sanusi II zuwa wajen bikin.

Kwankwaso ya ce ba ayi yarjejeniya ba

Mai shari’a John Okoro ya rusa hukuncin kotun daukaka kara da na sauraron korafin zabe inda APC mai adawa tayi galaba.

Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana kan zargin yin wani sulhu kafin Abba Kabir Yusuf ya iya samun nasara a kotu.

Tsohon gwamnan ya ce babu yarjejeniyar da aka shiga domin a bar NNPP a mulkin Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel