Kotun Koli: APC Sun Hango Nasara, 'Shirin' Rantsar da Gawuna Ya Kankama a Kano
- Magoya bayan jam’iyyar APC za su yi kwalliya iri daya idan za a rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna
- ‘Yan APC sun kwallafa rai a mulkin jihar Kano, su na ganin kotun koli za ta tsige Abba Kabir Yusuf
- Idan hakan ta faru, an yi dinkin riguna masu tambarin Tinubu wanda ‘yan APC za su a ranar a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kano - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta na kyautata zaton yin nasara kan NNPP a kotun koli a shari’ar zaben gwamnan jihar Kano.
Premium Times ta ce magoya bayan APC na reshen Kano sun fara rabon ankon kayan da za a sa ranar rantsar da Nasiru Yusuf Gawuna.

Kara karanta wannan
Watakila Kotun koli ta yanke hukunci a shari’ar zaben Gwamnan Kano nan da kwana 5

Source: Twitter
Ana addu'a domin Abba ya rasa mulkin Kano
Hakan yana zuwa ne bayan ‘ya ‘yan APC sun yi azumi da salloli da addu’o’i domin su sake samun galaba a kan Alhaji Abba Kabir Yusuf.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce tun a karshen makon jiya mabiya APC su ka fara rabon kayan anko a yankin Fagge a birnin Kano domin shirin rantsuwa.
‘Yan APC sun ci burin cewa Nasir Gawuna zai zama gwamna bayan tsige Abba Gida Gida a kotun koli, inda gwamnan ya daukaka kara.
Ana tunanin cikin makon nan alkalan kotun koli za su raba gardamar shari’ar zaben Kano.
'Yan APC a Kano sun yi dinkin ankon Gawuna
Wani Faisal Ibrahim ya ce ya yi dinkin kayansa kamar sauran ‘yan APC, su na jiran lokacin da za a rantsar da Gawuna ya zama sabon gwamna.

Kara karanta wannan
Bidiyon matashi da aka kama bisa zargin kashe mahaifinsa a Kano bayan caka masa wuka
Faisal Ibrahim yana ganin alkalan kotun koli za su ba lauyoyin jam’iyyar APC gaskiya.
Jagororin APC a Fagge irinsu Ahmad Dangwarzo sun raba wannan anko, sun ce idan dai ba a canza tsarin mulki ba, APC ta karbe mulkin Kano.
..."Abba ya tafi kenan"
Legit ta fahimci akwai wadanda su ka tanadi rigunan GawunaHasArrived G & G da za a ci kwalliya da su idan za a rantsar da sabon gwamna.
A bayan wadannan riguna an rubuta Sashe na 177, ma’ana sashen dokar da kotun daukaka kara tayi amfani da shi wajen tsige Abba a 2023.
Tsige Abba ya haifar da zanga-zanga
Ana da labari kotun korafin zabe da na daukaka kara sun ba Nasir Gawuna nasara a zaben Kano da aka yi a 2023, aka rusa nasarar NNPP mai-ci.
A dalilin hakan ne zanga-zangar lumana su ka barke a wasu wurare a jihar Kano.
Asali: Legit.ng