Gwamna Abba, Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Sun Hadu a Kano

Gwamna Abba, Kwankwaso da Mataimakin Shugaban Kasa, Shettima Sun Hadu a Kano

  • Matimakin shugaban Najeriya ya kaddamar da wani gini da aka gyara a ofishin Gwamnan jihar Kano
  • Kashim Shettima ya je Kano ne domin halartar jana’izar Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba a makon nan
  • Sanata Shettima ya hadu da tsohon gwamna kuma jigon NNPP watau Rabiu Kwankwaso a zuwansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Matimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da ofishin Mai girma gwamna da aka sake gyarawa a jihar Kano.

Sanarwa ta fito daga shafin hadimin Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim cewa Kashim Shettima ya kaddamar da ginin ranar Laraba.

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano tare da Kashim Shettima Hoto: Salisu Yahaya Hotoro
Asali: Facebook

Abdullahi Ibrahim a jawabin da ya fitar a X, ya ce Kashim Shettima ya bude ginin tare da shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas.

Kara karanta wannan

Awanni da mutuwar gwamna da tsohon Shugaban Majalisa, an rasa mai mulki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi gyara a ofishin Gwamnan Kano

Sauran wadanda su ka taya shi su ne: Mai girma Sanata Barau Jibril, Sanata Kawu Sumaila da mataimakin gwamna, Aminu A. Gwarzo.

Ginin da aka sabunta yana kunshe da zauren majalisar zartarwa, dakin taro da katafaren daki na musamman da ke gidan gwamnati.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta NAN ta ce Shettima ya yabawa gwamnan jihar Kano a kan yadda aka aiwatar da aikin da wuri.

Mataimakin shugaban kasar ya ce samar da gini na zamani irin wannan zai taimaka wajen jin dadin aikin ma’aikatan ofishin gwamnan.

“Ina taya Gwamna Yusuf da ‘yan majalisarsa murna a kan aikin da su ka yi da kyau.”

- Kashim Shettima

Kashim Shettima ya zo jana'iza

Salisu Hotoro, wani mai taimakawa Mai girma gwamnan da shawara ya ce Shettima ya zo garin Kano ne domin halartar jana’iza.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasar da su ka karbi mulki sanadiyyar mutuwar Gwamnonin jihohinsu a tarihi

"Mai girma gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya karɓi bakuncin mataimakin shugaban kasa Alh. Kashim Shettima wanda ya zo Kano domin gaisuwar tsohon kakakin majalisar dokoki ta ƙara Hon. Ghali Umar Na'abba wanda Allah yayiwa rasuwa a daren jiya."

- Salisu Hotoro

Tarihin gyaran gidan gwamnati

Wani rahoto da aka fitar ya nuna a shekarar 1967 aka fara gina ofishin a sa’ilin da Abdu Bako yake gwamnan jihar Kano a mulkin soja.

Mai girma Abdullahi Ganduje ya yi wasu gyare-gyare a ofishin mataimakin gwamnan Kano da ya karbi mulki a shekarar 2015.

Bidiyon Kwankwaso da Kashim Shettima

Legit ta ga bidiyo cewa Rabiu Musa Kwankwaso PhD FNSE ya hadu da Shettima da sauran musulmai a wajen jana’izar Ghali Na' Abba.

Sauran wadanda su ka halarci jana’izar sun hada da tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Kano tayi rashin Ghali Na'abba

Rahotanni sun zo a baya cewa Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba ya rasu a safiyar Laraba kuma an birne shi tun a jiya a mahaifarsa ta Kano.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaba Tinubu ya dira a jihar arewa bayan kashe bayin Allah sama da 100

Rt. Hon. Ghali Umar Na'abba ya rasu a birni Abuja ne yana shekara 65 da haihuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel