‘Yan Siyasar da Su Ka Karbi Mulki a Sanadiyyar Mutuwar Gwamnonin Jihohinsu a Tarihi

‘Yan Siyasar da Su Ka Karbi Mulki a Sanadiyyar Mutuwar Gwamnonin Jihohinsu a Tarihi

  • Shehu Kangiwa yana kan mulki ne ya rasu a wajen wasan folo, sai aka nada Garba Nadama a Junairun 1982
  • Da aka dawo mulkin farar hula, Ibrahim Geidam ya zama Gwamna da rashin lafiya ya kashe Mamman B. Ali
  • Mutuwar Gwamnan Kaduna ce ta sa Mukhtar Ramalan Yero ya yi shekaru uku yana mulki daga 2012 zuwa 2015

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Rahoton nan ya kawo jerin ‘yan siyasan da kaddara ta sa su ka zama Gwamnonin jihohi saboda mutuwar masu gidansu.

An fara samun irin haka ne tun a jamhuriya ta biyu a lokacin mulkin Shehu Shagari.

Gwamnonin kaddara a tarihi:

1. Garba Nadama

A sanadiyyar rasuwar Shehu Kangiwa, sai aka rantsar da Garba Namada a matsayin gwamnan jihar Sokoto a farkon shekarar 1982.

Kara karanta wannan

An hada tsohon shugaba Buhari da aiki a Katsina, watanni 7 da barin kujerar mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Garba Namada bai dade a ofis ba sai Muhammadu Buhari ya hambarar da gwamnatin farar hula, sojoji su ka karbi mulki.

Gwamnoni
Mataimakan Gwamnonin da su ka zama Gwamnoni Hoto: Inside_Yobe, Suleiman Abdullahi Rigachikun
Asali: Facebook

2. Ibrahim Geidam

Bayan rasuwar Mai girma Mamman Bello Ali a Amurka, wanda ya zama gwamnan jihar Yobe shi ne Ibrahim Geidam a shekarar 2009.

Bayan shafe shekaru goma yana mulki, Geidam ya zama Sanatan Yobe ta gabas a majalisa, yanzu Minista harkokin ‘yan sanda ne.

3. Ramalan Yero

Dallatun Zazzau, Mukhtar Ramalan Yero ne ya zama gwamna a Kaduna da Patrick Ibrahim Yakowa ya mutu a wani hadarin jirgin sama.

Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ya yi shekaru kusan uku a ofis sai aka yi zabe a 2015, a lokacin ne Nasir El-Rufai ya samu mulkin Kaduna.

4. Garba Umar/Sani Danladi

A lokacin da Danbaba Suntai ya kwanta rashin lafiya bayan hadarin jirgi, Garba Umar ya zama gwamnan riko saboda shi ne mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Awanni da mutuwar gwamna da tsohon Shugaban Majalisa, an rasa mai mulki a Najeriya

Da Danbaba Suntai ya rasu a 2017, sai kotun koli ta tsige Umar, aka dawo da tsohon mataimakin gwamna, Sani Danladi a kan kujerarsa.

5. Lucky Ayedatiwa

Kamar yadda ku ka samu labari a yammacin ranar Laraba, an rantsar da Mai girma Lucky Ayedatiwa a matsayin sabon gwamnan jihar Ondo.

Mista Ayedatiwa ya karbi mulki ne bayan rasuwar Gwamnan jihar watau Rotimi Akeredolu wanda ya yi watanni yana jinya a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel