Muhimman abubuwa 7 da ya dace a sani game da Kashim Shettima, abokin tafiyar Tinubu

Muhimman abubuwa 7 da ya dace a sani game da Kashim Shettima, abokin tafiyar Tinubu

  • 'Dan takarar kujerar shugabancin kasa a karkashin APC, Bola Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyarsa
  • Bayan Tinubu ya yi wannan sanarwar, 'yan Najeriya zasu so sanin karin bayani game da wannan 'dan siyasan haifaffan jihar Borno
  • Shettima makusancin Tinubu kuma 'dan gani-kasheninsa, mai masa yakin neman zabe tun kafin ya ci zaben fidda gwani na jam'iyyar APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A ranar Lahadi 10 ga watan Yulin 2022 ne 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Sanata Kashim Shettima na Borno a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu ya tabbatar da zabin Shettima a yayin zantawa da manema labarai a garinsu shugaban kasa Muhammadu Buhari, Daura dake jihar Katsina.

Kashim Shettima
Muhimman abubuwa 7 da ya dace a sani game da Kashim Shettima, abokin tafiyar Tinubu. Hoto daga Borno State Government
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Shettima bai san shine abokin takarata ba, in ji Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan takarar jam'iyyar APC ya je har garin Daura ne domin mika gaisuwar sallah babba da aka yi a ranar Asabar ga shugaban kasa.

Legit.ng ta zakulo muku tare da nemo muku muhimman abubuwan da ya dace ku sani game da 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC a zaben 2023.

  1. An haifa Shettima a Maiduguri dake jihar Borno a ranar 2 ga watan Satumban 1966 a gidan Sir Kashim Ibrahim. A halin yanzu yana da shekaru 55 a duniya kuma kabilar Kanuri ne.
  2. Tsohon gwamnan jihar Borno ne wanda ya mulka jihar tsakanin 2007 zuwa 2015 kuma Sanata ne mai ci a yanzu wanda aka zaba tun 2015 domin ya wakilci mazabar Borno ta tsakiya a majalisar dattawa.
  3. Yana da digirinsa na farko daga jami'ar Maiduguri inda ya karanci tattalin arziki na harkar noma da kiwo kuma yayi digirin digo a wannan fannin daga jami'ar Ibadan.
  4. Ya yi hidimar kasarsa a tsohon bankin manoma na Najeriya dake Kalaba, babban birnin jihar Cross River daga 1989 zuwa 1990.
  5. Shettima ya koma jami'ar Maiduguri a matsayin malami mai koyarwa a sashin tattalin arziki na noma da kiwo kuma ya kwashe shekaru 2 yana aikin.
  6. Shettima kwarraren ma'aikacin banki ne kuma masani a fannin tattalin arziki kafin ya fada siyasa. Daga 2007 zuwa 2011, ya rike kwamishina a ma'aikatu biyar.
  7. Yana auren Nana Shettima kuma sun haifa yara uku. Mata biyu da yaro namiji daya.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Masari ya janye daga matsayin abokin takarar Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel