Atiku Abubakar Ya Fadin Abin da Ya Kamata Abba Ya yi Bayan Harin Masallaci a Kano

Atiku Abubakar Ya Fadin Abin da Ya Kamata Abba Ya yi Bayan Harin Masallaci a Kano

  • Tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana harin masallacin garin Gadan da ke karamar hukumar Gezawa a Kano da tsantsar rashin imani
  • Ya bayyana haka ne ta cikin sakonnin da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, facebook da X, tare da bayyana cewa ya na cike da alhinin rashin da aka tafka
  • Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta gaggauta daukar matakin shari’a kan matashin da ya aikata danyen aikin, tare da tabbatar da an hukunta shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Tsohon shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana kaduwa kan harin da Shafi’u Abubakar ya kai kan masallata a garin Gadan dake karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Kara karanta wannan

"Gwamnatin Bola Tinubu ta jefa Najeriya cikin tsaka mai wuya," Dattijon Arewa

A makon da ya gabata ne matashin ya watsawa masallata kimanin 23 fetur, sannan ya cinna musu wuta a Larabar Abasawa da ke jihar ana cikin sallar asuba.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya nemi a binciki harin masallacin Kano Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana harin da mummunan aiki da bai kamata a ce ana samun irinsa a cikin al’umma ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya nemi binciken harin masallaci

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta gaggauta gudanar da binciken kwakwaf kan harin masallacin garin Gadan.

Zuwa yanzu, kimanin mutane akalla 15 ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu ke ci gaba da karbar magani a asibitin kwararru na Murtala da ke jihar.

A kalamansa:

“Ina mika sakon ta’aziyya ga iyalai da kuma ‘yan uwan wadanda wannan iftila’i ya rutsa da su.”

Kara karanta wannan

'Za a hada kai': Atiku ya bude baki a karon farko bayan zama da Peter Obi

Atiku Abubakar ya bayar da shawarar gaggauta daukar matakin shari’a a kan wadanda ake zargi da aikata laifin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.

Harin Kano: An kara samun wasu sun mutu

Mun kawo mu ku labarin yadda aka samu karin wadanda su ka riga mu gidan gaskiya a harin garin Gadan da wani matashi, Shafi’u Abubakar ya kai kan masallata da asubahi.

A lokacin da ya kai harin, ba a samu rashin rayuka ba, amma daga baya bayan an kai su asibitin kwararru na Murtala, mutanen su ka fara mutuwa daya da daya har adadinsu ya haura 15.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.