Tsohon Shugaban APC Ya Haddasa Fitina, Ya Fadi Yadda Aka Kashe N800m Saboda a Doke PDP

Tsohon Shugaban APC Ya Haddasa Fitina, Ya Fadi Yadda Aka Kashe N800m Saboda a Doke PDP

  • Adams Oshiomhole ya ce a lokacin da yake shugaban APC na kasa, sun kashe kudi domin a karbe jihohin PDP
  • Jihar Kwara ta na cikin wuraren da jam’iyyar APC ta maida hankali kansu a 2019 saboda ayi waje da Bukola Saraki
  • Jin Oshiomhole yana bayanin yadda APC ta kashe N800m a lokacin zabe ya jawo abin magana daga bangarori

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja A wajen nuna kokarin da ya yi a ofis, Adams Oshiomhole ya fadi yadda jam’iyyar APC ta kashe miliyoyi domin karbe jihar Kwara.

Da yake jawabi wajen kaddamar da littafin Salihu Lukman, Adams Oshiomhole ya ce uwar jam’iyya ta kashe N800m domin a doke APC a Kwara.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa farin jinin Tinubu yake raguwa tun da ya gaji Buhari - Jigon APC

Shugaban APC
APC ta dage sai da aka kifar da Bukola Saraki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jam’iyyar APC ta batar da wadannan kudi ne da nufin hambar da daular Bukola Saraki wanda ya sauya-sheka daga APC zuwa PDP a 2018.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP tana so a binciki jam'iyyar APC

Bayan maganar da tsohon shugaban na APC ya yi, Legit ta samu labari jam’iyyar PDP ta bukaci a kama APC da laifin sayen kuri’u yayin zabe.

Jam’iyyar hamayyar ta soki yadda APC tayi bindiga da daruruwan miliyoyi domin kurum tayi nasara a jihar Kwara a zaben da aka yi a 2019.

A karshe Abdulrazaq Abdulrahman da ‘yan takaran APC sun samu galaba a Kwara.

'Yan APC sun taso jam'iyya a gaba

Daily Trust ta rahoto Ibrahim Akaje yana neman a dawo masa da kudin da ya kashe wajen sayen fam domin shiga takarar majalisar tarayya.

Akaje ya bukaci a maido masa kudin da ya batar a 2019 ne bayan jin Oshiomhole yana cewa sun maidawa masu neman takara kudinsu.

Kara karanta wannan

Sabon rikici zai kurdo jam’iyyar PDP, Atiku ya lula Dubai bayan shari’ar zabe

Tsohon kwamishinan kasuwanci, kirkire da fasaha na jihar Kwara ya yi magana a Facebook, yana tambayar ina kudin na su suka shiga.

Ina shugabannin jam'iyyar APC?

Da jaridar ta tuntubi shugaban APC a Kwara, Alhaji Tajudeen Folaranmi Aro, ya ce yana wajen taro ne a lokacin, zai yi magana daga baya.

‘Dan siyasar ya ce tun da NWC ta ba jam’iyya ta reshen Kwara N800m da kuma N220m na kudin masu sayen fam, dole kudinsu su dawo.

Jigo ya jero matsaloli a mulkin APC

An samu labari Salihu Muhammad Lukman ya ce da farko Shugaba Bola Tinubu da APC sun samu karbuwa sosai wajen ‘yan Najeriya.

Jigon na APC ya ce yanzu an koma gidan jiya a jam’iyyar APC, sabon shugaban kasar ya koma irin mulkin da Muhammadu Buhari ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel