Oshiomhole Ya Fadi Mutane 3 da Su Ka Kore Shi Daga Shugabancin APC da Karfi da Yaji

Oshiomhole Ya Fadi Mutane 3 da Su Ka Kore Shi Daga Shugabancin APC da Karfi da Yaji

  • Adams Oshiomhole ya bada labarin yadda gwamnonin jihohi su ka huro wuta har ya rasa shugabancin jam’iyyar APC mai-ci
  • ‘Dan siyasar yake cewa akwai hannun Dr. Kayode Fayemi da Ibikunle Amosun wajen tsige shi da aka yi daga APC-NWC
  • Sanata Oshiomhole ya zargi gwamnonin lokacinsa da neman nuna masa yadda zai jagoranci APC alhali shi ne shugaba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Adams Oshiomhole ya bada labarin abubuwan da su ka je su ka dawo, har ya rasa kujerar shugabancin jam’iyyar APC na kasa.

Premium Times ta kawo rahoto cewa Adams Oshiomhole ya yi jawabi wajen kaddamar da littafin Salihu Lukman game da APC.

Adams Oshiomhole Fayemi Amosun
Adams Oshiomhole ya bar shugabancin APC Hoto: @KFayemi, @ siamosun da @nigeriagov
Asali: Twitter

Tsohon shugaban na APC kuma Sanatan Arewacin jihar Edo ya shaidawa kowa yadda gwamnonin jihohi su kayi sanadin rasa kujerarsa.

Kara karanta wannan

Zai Kawo Matsala: Yanzu ne Lokacin da Shugabanni Za Su Kora Wike Daga PDP - Hadimin Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oshiomhole ya kama sunayen Fayemi da Amosun

Rahoton ya ce Oshiomhole ya yi magana na kusan awa daya inda ya ce Kayode Fayemi da Ibikunle Amosun su ka hana shi sakat a APC.

Tsohon gwamnan na Edo ya zargi wadannan mutane biyu da sabawa doka wajen ganin an yi waje da shi daga matsayin shugaban jam’iyya.

A cewar Oshiomhole, gwamna Amosun ya fada masa cewa in ba domin Muhammadu Buhari ba, da tuni ya sauya-sheka daga APC.

"Ni ma tsohon Gwamna ne" - Oshiomhole

Tsohon gwamnan ya tunkari gwamnonin biyu, ya tuna masu cewa shi ma ya yi mulki na shekaru takwas a jere ba tare da canza gida ba.

A lokacin da abin ya faru, gwamnan Ekiti watau Kayode Fayemi shi ne shugaban NGF. The Cable ta ce Muhammadu Buhari bai sa baki ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya fadawa Ganduje muhimmin abin da Tinubu yake bukata wajensa

Adams Oshiomhole ya dura a kan Gwamnoni

Oshiomhole wanda yanzu yake majalisar dattawa ya zargi gwamnonin jihohi da kokarin nuna masa yadda zai gudanar da sha’anin APC.

A dogon bayaninsa, Sanatan ya ce kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta PGF ta nada Alhaji Salihu Lukman ne ba tare da an tuntube shi ba.

Salihu Lukman yana cikin wadanda su ka yaki shugaban APC na wancan lokacin.

Kayode Fayemi ya yi kira ga shugaban APC

A rahoton nan, Kayode Fayemi ya ce dole Abdullahi Umar Ganduje su rika fadawa Shugaba Bola Tinubu gaskiyar yanayin da al’umma ke ciki.

Tsohon gwamnan na Ekiti ya fadawa shugaban APC ya guji yi wa shugaban kasa zakin baki a Aso Rock, yace dole a fito da muradun jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel