Sabon Rikici Zai Kurdo Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Lula Zuwa Dubai Bayan Shari’ar Zabe
- Sule Lamido ya yi Allah-wadai da yadda abubuwa su ke tafiya a jam’iyyarsa ta PDP a karkashin jagorancin ‘yan NWC
- A ra’ayin tsohon gwamnan Jigawa, sakacin shugabannin jam’iyyar PDP ya jawo Bola Tinubu yana katsalandan a Ribas
- Idan za a bi ta Sule, akwai bukatar Iliasu Damagum da mutanensa su sauka daga mukaman da su ke kai a halin yanzu
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya fito ya fara maganganu game da halin da jam’iyyar PDP ta ke ciki a yau.
Alhaji Sule Lamido ya bukaci shugabannin jam’iyyarsu ta PDP na matakin kasa su sauka daga kujerunsu, ya yi kiran ne a Facebook.

Kara karanta wannan
Nazarin Shekarar 2023: Peter Obi, Kwankwaso da ‘Yan siyasa 6 da suka fi kowa tasiri a shekarar 2023

Asali: Twitter
Sule ya soki PDP NWC a kan rikicin Ribas
‘Dan siyasar ya nuna idan har PDP ba za ta iya kare Siminalayi Fubara a rikicinsa da Nyesom Wike ba, majalisar NWC ta gaza aikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani dogon jawabi da ya yi a shafinsa a dandalin na Facebook a ranar Laraba, ya ce bai kamata a zura ido a rikicin jihar Ribas ba.
Tsohon Ministan harkokin wajen kasar ya ba Gwamna Simi Fubara shawara ya yi watsi da yarjejeniyar da aka dauka a Aso Villa.
"Shin PDP ta na da kwamitin gudanarwa na kasa, ko kuwa dai a ce muna da wata jam’iyya mai suna PDP har yanzu?
Idan muna da daya daga cikin biyu, ta ya ba su nan a abin da yake faruwa da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP a Ribas?"
- Sule Lamido

Kara karanta wannan
Atiku, Amaechi, Shekarau, Binani da jiga-jigan ‘yan siyasa da suka fi kowa asara a 2023
Sule wanda yana cikin kwamitin amintattu ya ce abin kunya ne yadda aka bari shugaban kasa ya tsoma masu baki a jihar Ribas.
Matashi 'dan PDP ya ce a kori NWC
Adnan Mukhtar Tudun Wada wanda matashin ‘dan jam’iyyar PDP ne a reshen Kano ya ce shakka babu akwai bukatar ta sake zani.
Malam Adnan Tudun Wada yana cikin masu goyon bayan Iliasu Damagum su yi waje, ya fadawa Legit wannan a safiyar Juma’a.
‘Dan siyasar ya zargi Damagum da majalisarsa da yi wa Nyesom Wike aiki, yake cewa ba su dace a bar jam’iyya a hannunsu ba.
"Ya kamata a kira karamin gangami, su canza Damagum da wanda ya cancanta ya jagoranci ja’iyyar nan yadda ya dace."
- Adnan Mukhtar Tudun Wada
PDP: Ina Atiku Abubakar?
A duk abubuwan nan da ke faruwa, Legit ta na zargin Alhaji Atiku Abubakar wanda shi ne jagoran jam’iyyar adawar yana kasar waje.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu da wasu jiga-jigai na cikin matsala, Shugaban PDP na ƙasa ya ɗau zafi
Dino Melaye ya fito da wasu hotuna da ke nuna ‘dan takaran na PDP ya tafi birnin Dubai.
Asali: Legit.ng