Wani hani daga Allah Baiwa ne: Mun ji dadi da Saraki ya bar APC – Lai Mohammed

Wani hani daga Allah Baiwa ne: Mun ji dadi da Saraki ya bar APC – Lai Mohammed

Alhaji Lai Mohammed wanda shi ne Ministan yada labarai na kasar nan yayi magana game da siyasar Najeriya a lokacin da aka yi hira da shi a wani shiri mai suna ‘Stepping Up’ a gidan Talabijin na NTA.

Lai Mohammed ya nuna cewa yana goyon bayan zaben kato-bayan-kato da Jam’iyyar APC ke kokarin kawowa a zaben 2019. Ministan yace hakan ne zai ba da dama Jam’iyyar ta ba ‘Yan takarar da su ka fi shahara tuta a zaben da za ayi.

Ministan labarai da ala’adun kasar Mohammed ya kuma yi magana game da batun sauya-shekar da ake gani inda yace ana zuzuta lamarin. Mohammed yace ficewar Bukola Saraki da mutanen sa daga APC ya zama alheri a Jihar Kwara.

Babban Ministan yake cewa duk da Jam’iyyar APC mai mulki ta jijjiga lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa ya koma PDP, hakan ya zama alheri ga Jam’iyyar domin kuwa wasu manyan PDP sun soma dawowa APC bayan tashin Saraki.

KU KARANTA: Abin da ya sa Kasashen Duniya ke durowa Najeriya – Lai Mohammed

Kwanaki ne Shugaban Majalisar Kasar tare da Gwamnan Jihar Kwara da kuma kusan kaf ‘Yan Majalisun Jihar Kwara su ka sauya-sheka zuwa Jam’iyyar PDP. Ministan kasar Lai yace wasu da su ke jiran Saraki ya bar APC yanzu sun bar PDP.

Tsohon babban Sakataren yada labaran na Jam’iyyar APC Alhaji Lai ya nuna cewa Jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Jihar Kwara a 2019. Ministan labarai da al’adun na Najeriya yace yana da cikakken yakinin cewa Jam’iyyar su za ta yi nasara.

Kwanaki kun ji labari cewa Ministan yada labarai na Gwamnatin Najeriya yayi kaca-kaca Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki wanda yace bai taba marawa tafiyar Shugaba Buhari baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng