A Karshe, Jam'iyyar PDP Ta Fara Ɗaukar Matakan Farfaɗowa Daga Bugun da Ta Sha a Zaben 2023

A Karshe, Jam'iyyar PDP Ta Fara Ɗaukar Matakan Farfaɗowa Daga Bugun da Ta Sha a Zaben 2023

  • Babbar jam'iyyar adawa ta fara ɗaukar matakan magance matsalolin cikin gida da suka haɗa mambobinta faɗa
  • A taron kwamitin gudanarwa (NWC) na ƙasa, PDP ta umarci 'ya'yanta su janye ƙararrakin da suka shigar a gaban kotu
  • Rigingimun cikin gida na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ake ganin sun kassara PDP a zaben da ya wuce

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Peoples Democratic Party (PDP) ta ƙasa ta umarci dukkan mambobi su gaggauta janye duk wata ƙara ta suka shigar a gaban kotu kan rikicin cikin gida.

Babbar jam'iyyar adawar ta bada wannan umarni ne ranar Talata, 5 ga watan Disamba, 2023 a Abuja a wani yunƙuri na warware duk wani rikicin cikin gida.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka dasa bam a babbar jami'ar Najeriya, yan sanda sun yi bayani

Jam'iyyar PDP ta fara ɗaukar matakai.
Jam'iyyar PDP Ta Fara Yunkurin Farfadiwa Daga Rigingimun Cikin Gida da Suka Addabe Ta Hoto: OfficialPDP
Asali: UGC

Jaridar Leadership ta tattaro cewa umarnin na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP na ƙasa, Mista Debo Ologunagba, ya fitar bayan taron NWC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kaɗan bayan kammala taron kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP, Ologunagba, ya ce kwamitin ya bada umarnin janye ƙararrakin ne bayan nazarin halin da jam'iyya ke ciki.

Meyasa PDP ta ɗauki wannan matakin?

Ya kara da cewa umarnin da NWC ya bayar ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP da aka yi wa garambawul a shekarar 2017.

Haka nan kuma ya ce janye ƙararrakin na faɗa da juna tsakanin 'ya'yan PDP zai taimaka wajen tabbatar da hadin kai da sulhu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kakakin PDP ya ce:

"Kwamitin NWC ya roƙi daukacin jagororinn jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da mambobi su hada kan su wuri ɗaya, su ci gaba da yaɗa manufofin PDP, jam’iyyar dimokuradiyya ta gaskiya."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar Labour Party ta caccaki Peter Obi, bayanai sun fito

Ologunagba ya kara da bayanin cewa NWC ya kuma yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin da aka kafa domin nadin babban darakta-janar na Cibiyar Dimokuradiyya ta PDP.

Idan baku manta ba, rikicin cikin gida na ɗaya daga cikin dalilan da ake hasashen sun jawo wa PDP faɗuwa a babban zaɓen 2023.

Zamu tabbata an yi adalici - Sanatan Kaduna

A wani rahoton na daban Sanata Sunday Marshall Katung ya ce zasu tabbata an yi wa mutanen da harin bam ɗin sojoji ya shafa adalci.

Katung, Sanata mai wakiltar Kaduna ta kudu ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu a kauyen Tudun Biri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262