Jiga-Jigai da Magoya Bayan Tsohon Gwamna Sun Fice Daga Jam'iyya, Sun Koma Jam'iyyar PDP Kan Abu 1

Jiga-Jigai da Magoya Bayan Tsohon Gwamna Sun Fice Daga Jam'iyya, Sun Koma Jam'iyyar PDP Kan Abu 1

  • Jam'iyyar PDP ta fara farfaɗowa a jihar Ekiti yayin da wasu ɗaruruwan mambobi da jiga-jigan SDP suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar
  • Masu sauya shekar waɗanda suka kasance magoya bayan tsohon gwamna, Segun Oni, sun rungumi PDP ranar Litinin
  • Sun bayyana cewa a shirye suke su bada gudummuwa wajen ganin PDP ta dawo kan ganiyarta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Ɗaruruwan mambobi da magoya bayan Social Democratic Party (SDP) sun sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar adawa PDP a jihar Ekiti.

Jiga-jigan yan siyasan da suka sauya sheka zuwa PDP sun kasance magoya bayan tsohon gwamnan Ekiti kuma ɗan takarar SDP a zaben da ya gabata, Chief Segun Oni.

Kara karanta wannan

Daga karshe an bayyana dalilin da ya sanya PDP ta kasa hukunta Wike da yan G-5

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni.
Magoya Bayan Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti Sun sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP Hoto: Segun Oni
Asali: Facebook

Tawagar masu sauya sheƙar sun fito ne daga dukkan gundumomi 13 na karamar hukumar Ado, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabbin mambobin PDP sun sauya sheƙar ne karƙashin jagorancin tsohon shugaban jam'iyya a ƙaramar hukumar Ado, Yinka Olomofe da kuma Fatai Adeyemo.

Sun samu tarba mai kyau ranar Litinin daga manyan kuoshin PDP da suka haɗa da kakakin PDP na jihar, Chief Olalekan Amerijoye da na Kudu maso Yamma, Cif Olalekan Amerijoye da sauransu.

Meyasa suka zabi shiga PDP?

Da yake jawabi a madadin masu sauya sheƙa, Mista Olomofe ya ce a baya sun bar PDP zuwa SDP gabanin zaben gwamna na 2022 saboda rashin gamsuwa da harkokin ciki gida

Amma a cewarsa, yanzu suna farin cikin sake dawowa PDP kuma zasu yi aiki tuƙuru ba kama hannun yaro domin sake gina jam'iyyar gabanin babban zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe gawurtaccen ɗan bindigan da ya hana jama'a zaman lafiya a arewa

Olomofe ya kuma sanar da cewa gaba ɗaya ɗaya tsarin SDP ya rushe zuwa cikin PDP a ƙaramar hukumar Ado tunda suka yanke shawarin sauya sheƙa.

Da yake karbar sabbin mambobin, shugaban riko na PDP, Sodiq Obanoyen, wanda kakakin jam’iyya, Amerijoye ya wakilta ya yabawa tsaffin mambobin SDP bisa matakin da suka dauka na komawa PDP maimakon jam’iyya mai mulki.

Ya kuma tabbatar musu da cewa masu ruwa da tsaki na kan aikin sake farfaɗo da jam'iyyar PDP a Ekiti duba da kalubalen da take fuskanta, in ji rahoton Leadership.

EFCC na shan matsin lamba ta kama ministan Buhari

A wani rahoton na daban Jam'iyyar APC reshen Bayelsa ta zargi Gwamna Douye Diri da matsawa EFCC lamba ta kama tsohon minista, Timipre Tylva.

Mai magana da yawun APC na jihar, Buokoribo, ya ce Diri na kulla wannan makirci ne domin ya hango zai rasa kujerarsa a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel