Zaben Kano: Tinubu Ya Shiga Babbar Matsala Kan Tsige Gwamna Abba Gida-Gida

Zaben Kano: Tinubu Ya Shiga Babbar Matsala Kan Tsige Gwamna Abba Gida-Gida

  • Ƙungiyoyi da wasu jagororin siyasa sun gargaɗi shugaban kasa, Bola Tinubu, ya guji neman tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano
  • Wata kungiya mai rajin kawo ci gaba ta yi gargaɗin cewa sauke Gwamnan daga mulki ka iya tarwatsa siyasa da haɗin kan Najeriya
  • Kotun zaɓe ta tsige Gwamna Yusuf kana ta ayyana Nasir Gawuna a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Kano, yau Kotun ɗaukaka ƙata zata yi hukunci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na fuskantar matsin lamba kan ya amince da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kano wanda aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Abba Kabir Yusuf, Shugaba Tinubu da Gawuna.
Kano: An Matsa Wa Shugaba Tinubu Lamba Kan Tsige Abba Gida-Gida Daga Gwamna Hoto: Abba Kabir Yusuf, Bola Ahmed Tinubu, Nasir Gawuna
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu na shan matsin lamba kan kujerar gwamnan Kano ne domin daidaito da adalcin siyasa da kuma samun haɗin kai mai ɗorewa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun dauki mataki a wasu wurare a Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara ta tsige Gwamna Abba

A rahoton jaridar Leadership, wasu jagororin siyasa da ƙungiyoyi masu zaman kansu ne suka buƙaci haka ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne yayin da Kotun Daukaka Kara ke shirin yanke hukuncin ƙarshe kan ƙarar da ta kalubalanci hukuncin Kotun zaɓe wadda ta tsige Abba Kabir Yusuf.

Wata ƙungiya ta roƙi Shugaba Tinubu kan ƙarar zaben Kano

A wurin taron tattaunawa na ƙungiyar rajin kawo ci gaba (FNID) ƙarƙashin Oguntade Omolewa, ƙungiyar ta gargaɗi Tinubu ya daina bin haramtaciyar hanya da nufin tsige Abba Gida-Gida.

Yusuf, ɗan takarar jam'iyyar NNPP ya samu nasara kan babban abokin karawarsa na APC, Nasir Gawuna a zaben da ya gabata kuma INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓe.

A halin yanzu, Kotun ɗaukaka kara ta shirya yanke hukunci wanda zai zama raba gardama a karar da Gwamna Yusuf ya ɗaukaka yana kalulabalantar tsige shi da aka yi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Halin da mutane suka shiga a jihar Kano bayan kotun ɗaukaka ƙara Ta tsige Abba Gida-Gida

Hadimin Atiku ya yi hasashen hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara

A wani rahoton na daban Mai magana da yawun Atiku Abubakar, Abdulrasheed Shehu, ya yi hasashen wanda zai samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara kan zaben Kano.

Jigon jam'iyyar PDP ya bayyana cewa lissafin da ke gaban APC shi ne ta maida Najeriya hannun jam'iyya ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel