Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

Abba v Gawuna: An Ja Hankalin Bola Tinubu Kan Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano

  • Wasu kungiyoyi masu zaman kan su sun nuna rashin goyon bayan yin amfani da kotu wajen rusa zaben Gwamnan jihar Kano
  • Kungiyoyin sun bukaci shugaban kasa ya tabbata an yi adalci kuma an duba tsaron kasa wajen hukunci a kan shari’ar zaben
  • Tsohon ‘dan takaran shugaban kasa a 2019 ya ce Abba Kabir Yusuf aka zaba jihar Kano, bai kamata kotun zabe ta tunbuke shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Jagororin siyasa da kungiyoyi masu zaman kan su, sun roki Bola Ahmed Tinubu ya rungumi zaben gwamnan da aka yi a Kano.

A wani rahoto da ya fito a Leadership, an ji cewa Oguntade Omolewa ya jagoranci wata tattaunawa da aka yi kan harkar siyasa a Abuja.

Kara karanta wannan

Ka Canza Hali: Tsohon Shugaba a APC Ya Fadi Kuskuren Tinubu Daga Shiga Aso Rock

Zaben Gwamnan Kano
Ana shari'ar zaben Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Gawuna Hoto: @Kyusufabba, @AbubakarmusaDK1
Asali: Twitter

APC v NPP: Tinubu ya yi hattara da Kano

Matsayar da aka dauka bayan zaman shi ne ya kamata a guji amfani da kotuna wajen rusa zaben gwamnan Kano da NNPP ta lashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Yan siyasar sun ja kunnen Bola Tinubu kan hadarin ruguza zaben ta hanyar shari’a saboda jihar Kano ta zauna cikin kwanciyar hankali.

Cif Omolewa ya yi kira ga Mai girma shugaban kasa ya guji yin abin da zai kawo rabuwar kan al’ummarsa kuma ya zama mai tafiya da kowa.

Tun ba yau ba aka ji Sheikh Sani Ashir ya na cewa ana so a dawo da APC mulkin Kano.

'Dan takaran 2019 ya ce NNPP ta ci Kano

Jaridar ta ce ‘dan takaran shugaban kasa a tsohuwar jam’iyyar ANP, Moshood Shittu ya yi makamancin wannan gargadi ga shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Wasu sun sace wayar tsohon minista a kotu wajen sauraron shari’ar zabe

Shittu ya tunawa Tinubu abin da ya faru da shi a 2003, a cewarsa an kyale masa mulkin Legas duk da irin karfin PDP a gwamnatin tarayya.

‘Dan siyasan ya yi kira ga kotun daukaka kara ta duba maslahar tsaro da kishin kasa wajen zartar da hukuncin a shari’ar zaben na jihar Kano.

"Ba mu san rikicin siyasa a Kano, shiyasa mu ke kiran ayi adalci kuma ayi amfani da basira wajen zartar da hukunci.
Mutanen Kano sun fito kwansu da kwarkwatarsu sun zabi Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben gwamnonin jihohi na 2023.”

- Mashood Shittu

Sanata Shehu Sani ya na cikin manyan 'yan siyasar da ke ganin bai dace ayi amfani da kotu wajen karbe mulki daga hannun NNPP ba.

A zaben bana na 2023, hukumar INEC ta tabbatar da ‘dan takaran NNPP watau Abba Kabir Yusuf ne ya doke Dr. Nasiru Yusuf Gawuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel