Babbar Magana: An Roki Shugaba Tinubu Ya Kori NSA Nuhu Ribadu, Bayanai Sun Fito

Babbar Magana: An Roki Shugaba Tinubu Ya Kori NSA Nuhu Ribadu, Bayanai Sun Fito

  • An fara kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan ya tsige Nuhu Ribadu a matsayin mai bada shawara kan tsaro saboda furucinsa na baya-bayan nan
  • A wajen wani taro, tsohon shugaban na EFCC ya fito fili ya caccaki gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta gaji tsiya daga gwamnatin baya, cewa shine dalilin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki

FCT, Abuja - An shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya tsige babban mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu.

Wannan kira na kunshe ne a cikin wani rubutun ra’ayi da wani marubuci mazaunin Abuja, Abbah Modibo ya yi a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: "Mun kama waɗanda suka jibgi shugaban NLC" NSA ya aike da sako ga kungiyoyin kwadago

An nemi a tsige Nuhu Ribadu a matsayin NSA
An Nemi Shugaba Tinubu Ya Tsige Nuhu Ribadu, Cikakken Bayani Ya Bayyana Hoto: Arewa Business Hub
Asali: Twitter

Kamar yadda yake kunshe a rubutun wanda Legit ta samu, Modibo ya bayyana cewa Ribadu bai cancanci rike wannan muhimmin mukami kamar da mai ba kasa shawara kan tsaro ba.

Ya bayyana dalilinsa kan furucin da Ribadu ya yi cewa gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsiyata kasar kafin ta mika mulki ga Shugaba Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoto da Legit Hausa ta fitar a baya, an nakalto Ribadu yana cewa:

"Muna fuskantar cikas sosai wajen kasafin kudi. Zai yi kyau in fada maku. Zai yi kyau ku sani. Mu na cikin halin ha’ula’i.
"Mun gaji kasa mai wahalar sha’ani, kasa a tsiyace har ta kai mu na biyan bashin abin da aka dauka. Abin ya yi kamari.
"Amma gwamnatin nan ta na yin bakin kokarinta wajen ganin mun sauke nauyin da ya rataya, daga ciki har da na sojoji."

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

Dalilin da yasa ya zama dole Tinubu ya kori Ribadu - Madibbo

Da yake martani kan furucin Ribadu, Madibbo ya ce:

"Idan har akwai wata hujja da ke nuna rashin sani da jahilcin Nuhu Ribadu, zarge-zargen da ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwanan nan ya tabbatar da hakan.
"A takaice Nuhu Ribadu bai dace da zama mutumin da zai riki ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba, kuma ya kamata a gaggauta sauke shi kafin ya jefa al'umma cikin mawuyacin hali."

Modibbo ya kuma bayyana cewa furucin Ribadu ya bai wa jam'iyyun adawa makamin da suke bukata don farfadowa daga rikcin cikin gida da suka fada.

Ya ce jawabin ya kuma ruguza “karin kokarin da shugaban jam’iyyar APC ke yi na gyara jam’iyyar.

Ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi wa tufkar hanci sannan ya gaggauta korar Ribadu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya tsiyata Najeriya kafin mikawa Bola Tinubu mulki Inji Nuhu Ribadu

Ribadu ya gana da yan kwadago

A wani labarin, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta shiga ganawa da kungiyoyin kwadago da suka hada da NLC da TUC don tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen yajin yajin gama gari da kungiyoyin suka shiga.

A cewar wani rahoto na NTA, taron yana gudana ne a ofishin Nuhu Ribadu, mai ba wa shugaban kasa Tinubu shawara kan harkokin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel