Yajin Aiki: "Mun Kama Waɗanda Suka Jibgi Shugaban NLC" NSA Ya Aike da Sako Ga Ƙungiyoyin Kwadago

Yajin Aiki: "Mun Kama Waɗanda Suka Jibgi Shugaban NLC" NSA Ya Aike da Sako Ga Ƙungiyoyin Kwadago

  • Gwamnatin tarayya ta roki ƙungiyoyin kwadago su janje yajin aikin da suka fara kan abin da aka yi wa shugaban NLC a jihar Imo
  • Mai ba da shawara kan tsaron kasa, Nuhu Ribaɗo, ya ce an kama waɗanda suka farmaki Ajaero kuma bincike ya yi nisa
  • A madadin FG, Ribaɗu ya roƙi ƴan kwadago su yi hakuri su dawo teburin tattauna wa domin lalubo maslaha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, ya nemi afuwar kungiyar kwadago kan harin da aka kai wa shugaban NLC, Joe Ajaero, a Owerri, babban birnin jihar Imo ranar 1 ga watan Nuwamba.

Malam Nuhu Ribaɗu, NSA ga shugaba Tinubu.
Yajin Aiki: "Mun Kama Waɗanda Suka Jibgi Shugaban NLC" NSA Ya Aike da Sako Ga Ƙungiyoyin Kwadago Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Abin da ya faru tun farko a Imo

Kara karanta wannan

To fa: Babbar matsala ta kunno kai, ta dakatar da sake gurfanar tsohon gwamnan CBN a Kotu

Mista Ajaero ya je Owerri ne domin ya jagoranci wata zanga-zanga, amma bisa rashin sa a aka lakaɗa masa dukan tsiya kuma aka tsare shi na tsawon awanni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka shugabannin ƙungiyoyin ma'aikata suka baiwa Gwamnati wa'adi ta biya musu wasu bukatu, ciki har da kama masu hannu a cin zarafin shugaban NLC.

Sun kuma yi barazanar tsaida ayyuka cik a faɗin Najeriya ta hanyar shiga yajin aiki idan ba a biya musu bukatunsu ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya ta garazaya Kotu domin dakatar da ma'aikatan, amma duk da haka suka fara yajin aikin sai baba ta gani ranar Talata, wanda ya kawo cikas a faɗin kasar nan.

NSA ya roƙi kungiyoyin NLC da TUC su yi hakuri

Ribaɗu ya roki ma'aikata su janye yajin aikin, a wata sanarwa da shugaban sashin sadarwa na ofishin mai bada shawara kan tsaro, Zakari U Mijinyawa ya fitar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya bayyana tarin gwaramar da shugabannin da suka gabacesa suka bar wa gwamnatinsa

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda suka farmaki shugaban NLC har suka lakaɗa masa duka sun shiga hannu kuma tuni aka fara bincike kan lamarin.

Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta yi nadamar abin da ya faru a Imo kuma ta yi Allah wadai da shi baki daya, rahoton The Cable ya tabbatar.

Wani sashin sanarwan ta ce:

“Bisa haka Gwamnatin Tarayya ta ofishin NSA, ta na kira ga shugabannin kwadagon da su janye yajin aikin da suke yi a yanzu, su rungumi tattaunawar da aka fara."

Yajin aikin NLC ya dakatar da shari'ar Emefiele

A wani rahoton na daban Yajin aikin ƙungiyar JASUN ya dakatar da shirin sake gurfanar da tsohon Gwamnan CBN a gaban babbar Kotun Abuja.

Kungiyar ma'aikatan shari'a ta umarci mambobinta su bi umarnin NLC su shiga yajin aikin sai baba ta gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel