Hadimin Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Zaben Bayelsa, Ya Aike da Sako Ga Gwamna Diri Na PDP

Hadimin Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Zaben Bayelsa, Ya Aike da Sako Ga Gwamna Diri Na PDP

  • Mai baiwa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya taya Gwamna Douye Diri na PDP murnar lashe zaɓen jihar Bayelsa
  • Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta ayyana Diri a matsayin wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan da aka yi ranar Asabar
  • Jim kaɗan bayan haka, Bayo Onanuga ya wallafa sakon murna tare da ambatar jam'iyyar PDP a shafinsa ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mai ba shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya aike da saƙon taya murna ga Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa.

Shugaba Tinubu da Gwamna Douye Diri.
Hadimin Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamna Diri Murnar Samun Nasara a Bayelsa Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Douye Diri
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasar ya taya Gwamna Diri na jam'iyyar PDP murnar lashe zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa wanda aka yi ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kogi: Ɗan takarar PDP ya ɗauki zafi, ya baiwa Hukumar INEC wa'adin kwana bakwai ta yi abu 1 tak

A yau Litinin, hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Sanata Diri, ɗan takarar jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri'u mafi rinjaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kaɗan bayan haka ne, tsohon mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Onanuga, ya tura saƙon taya murna ga Diri.

A wani gajerin saƙo da ya waallafa a shafinsa na Tuwita ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, 2023, Onanuga ya taya Diri murnar samun nasarar ta zarce a kujerarsa.

"Muna taya Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP murna bisa samun nasarar tazarce a kujerar Gwamnan jihar Bayelsa," in ji shi.

Shugaba Tiɓubu ya maida martani

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban Tinubu ya taya ɗaukacin zaɓaɓɓun Gwamnonin jihohin Bayelsa, Imo da Kogi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya bai wa asibiti gudunmawar naira miliyan 20, ya bayyana dalili

A jihar Imo, Gwamna Hope Uzodinma na APC ya samu nasara, Usman Ododo ya lashe zaɓen Gwamna a jihar Kogi yayin da Gwamna Diri ya zarce zango na biyu a Bayelsa.

Hadimin Shugaba Tinubu Ya Magantu Kan Zaben Bayelsa

A wani rahoton na daban Mai baiwa shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai ya taya Gwamna Douye Diri na PDP murnar lashe zaɓen jihar Bayelsa.

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta ta ayyana Diri a matsayin wanda ya samu nasara a zaben Gwamnan da aka yi ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel