Kogi: Ɗan Takarar PDP Ya Ɗau Zafi, Ya Baiwa Hukumar INEC Wa'adin Kwana Bakwai Ta Yi Abu 1 Tak

Kogi: Ɗan Takarar PDP Ya Ɗau Zafi, Ya Baiwa Hukumar INEC Wa'adin Kwana Bakwai Ta Yi Abu 1 Tak

  • Sanata Dino Melaye na PDP ya ce INEC na da wa'adin kwana bakwai ta duba ƙorafin da ya kai mata kan zaɓen Gwamnan jihar Kogi
  • Ɗan takarar Gwamna a inuwar PDP ya ce tuni ya miƙa kokensa ga INEC kan abubuwan da ya hango sun faru a lokacin zaɓe
  • Ya yi zargin cewa an tafka magudi, aringizon kuri'u da sauransu shiyasa ɗan takarar Yahaya Bello ya samu nasara

Jihar Kogi - Ɗan takarar Gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya bai wa hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) wa'adi ta duba kokensa.

Sanata Dino Melaye.
Zaben Kogi: Melaye Ya Baiwa INEC Wa'adin Mako Daya Ta Duba Korafinsa Hoto: Senator Dino Melaye
Asali: UGC

Sanata Melaye ya bayyana cewa wa'adin kwana Bakwai kacal ya ɗibarwa INEC ta sake nazari da duba kan zaɓen Gwamnan da aka kammala a jihar Kogi.

Ɗan takarar PDP wanda ya sha kaye hannun abokin hamayyarsa na APC, Usman Ododo, ya yi wannan furucin ne a hira da Channels tv cikin shirin siyasa a yau.

Kara karanta wannan

Hadimin Shugaba Tinubu ya magantu kan zaben Bayelsa, ya aike da sako ga gwamna Diri na PDP

A ranar Lahadi, hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Usman Ododo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya ci zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ododo ya samu kuri’u 446,237, yayin da babban abokin hamayyarsa, Murtala Ajaka na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya samu kuri’u 259,052.

Amma da yake jawabi a hirar, Melaye ya ce zaɓen cike yake da kura-kurai, aringizon kuri'u, da yi wa masu kaɗa kuri'a barazana.

Kwana 7 suka rage wa INEC

Daily Trust ta tattaro Sanata Melaye na cewa:

"A bisa maguɗin sakamakon ne aka ayyana dan takarar Yahaya Bello a matsayin wanda ya lashe zaben. INEC tana sane da cewa an rubuta wasu sakamakon kananan hukumomi tun kafin zaben."
"Haka ta faru a sauran kananan hukumomin, an yi aringizon ƙuri'u a kananan hukumomi 17. Mun mika kokenmu ga INEC yau da rana haɗe da hujjoji."

Kara karanta wannan

To fa: Wakilin APC ya tubure, ya faɗi abin da ka iya canza sakamakon zaben Gwamnan jihar Bayelsa

"Abu na gaba da zamu yi, zamu zura ido mu saurara, mun ba INEC kwanaki bakwai ta yi nazari a kan ƙorafin mu. Zamu jira mu ga wane mataki za su ɗauka."

Wakilin APC ya ƙi sanya hannu a jihar Bayelsa

A wani rahoton na daban Wakilin APC a cibiyar tattara sakamakon zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa, Dennis Otiotio, ya tubure ya ƙi sanya hannu a takardar sakamakon.

Mista Otiotio ya yi haka ne domin nuna rashin gamsuwa da kuma zargin an soke ƙuri'u 80,000 na APC a wasu akwatunan zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262