‘Yan Takara 7 Sun Hakura Sun Janye Yayin da Gwamnan Kogi Ya ‘Tsaida’ Magaji a APC

‘Yan Takara 7 Sun Hakura Sun Janye Yayin da Gwamnan Kogi Ya ‘Tsaida’ Magaji a APC

  • A yau ne APC za tsaida wanda zai yi mata takarar sabon Gwamna a jihar Kogi a zabe mai zuwa
  • Edward Onoja wanda shi ne mataimakin Gwamnan Kogi ya bada sanarwar fasa neman tikiti
  • Alamu na nuna Ahmed Usman-Ododo ne wanda Yahaya Bello yake so Jam’iyyar APC ta tsaida

Kogi - A Juma’ar nan jam’iyyar APC za ta shirya zaben tsaida gwani na ‘dan takarar Gwamna a jihar Kogi, a daren yau siyasar ta dauki wani salo.

Rahoton Premium Times ya tabbatar da cewa wasu daga cikin wadanda ake tunanin za su iya samun tikitin APC a jihar Kogi, sun janye takararsu.

Mai girma mataimakin Gwamna, Edward Onoja ya hakura da shiga zaben fitar da gwani na yau. Wasu sun yi tunanin shi zai samu takara a APC.

Kara karanta wannan

Makarkashiyar Gwamnonin PDP Ta Jawo Rikicin Cikin Gidan Jam’iyya Zai Koma Sabo

Onoja zai goyi bayan Ahmed Usman-Ododo wanda shi ne Mai binciken kudin gwamnatin Kogi.

Mutum 7 sun janyewa Ododo

Jaridar ta ce baya ga haka, wasu ‘yan takara bakwai sun fasa neman tikitin jam’iyya mai-ci ganin cewa Gwamna Yahaya Bello ya nuna ‘dan takaransa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana zargin Mai girma Yahaya Bello yana so Ahmed Usman-Ododo ya gaji kujerarsa ne a badi.

Gwamnan Kogi
Edward Onoja da Yahaya Bello Hoto: kogireports.com
Asali: UGC

Tsohon Kwamishinan kudi, David Adebanji-Jimoh da Ashiru Idris da kuma Okala Yakubu su na cikin masu neman takara a APC da yanzu sun sallama.

Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati, Abdulkareem Asuku ba zai shiga yakin neman tikitin ba, yana cikin wadanda ake ganin yana kusa da Gwamna.

Shi ma Akanta Janar na jihar Kogi, Momoh Jibrin ba zai shiga takarar da za a shirya a yau ba. NAN ta ce hakan na zuwa ne bayan taron yammacin Alhamis.

Kara karanta wannan

"PDP Ba Za Ta Kai Labari Ba Idan Har Ta Ba Dino Melaye Tikitinta a Zaben Gwamnan Kogi", Wike

Gwamna Bello ya jagoranci zama da wadanda ke harin kujerarsa a sakatariyar APC da ke Lokoja.

Bello Matawalle ya yi magana

A rahoton da This Day ta fitar, shugaban kwamitin zaben tsaida gwanin, Gwamna Mohammed Bello-Matawale ya tabbatar da haka bayan taron na jiya.

Mohammed Bello Matawalle ya ce wadanda ba su janye ba za sui ya shiga zaben. Irinsu Edward Onoja sun fitar da sanarwa game da batun a Facebook.

Tinubu: Na shiga uku - Sinatu Ojikutu

An ji labari Sinatu Aderoju Ojikutu ta fi shekaru 20 ana ‘yar tsama tsakaninta da Bola Tinubu, ta ce za ta tashi daga ‘Yar Najeriya kafin rantsar da sabon Shugaban.

Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnar ta goyi bayan Peter Obi ne a zaben shugaban Najeriya, yanzu 'yar siyasar ta ce rayuwarta tana cikin mummunan hadari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel