Zaben Gwamnan Kogi: Abubuwan da Za a Sani Kan Dino Melaye da Manyan 'Yan Takara 4

Zaben Gwamnan Kogi: Abubuwan da Za a Sani Kan Dino Melaye da Manyan 'Yan Takara 4

  • Nan da ‘yan kwanaki kadan ake sa ran Hukumar INEC za ta sanar da wanda ya zama sabon Gwamnan jihar Kogi
  • Wannan karo ba manyan jam’iyyu irinsu APC da PDP kurum ake yi wa hangen nasara ba, akwai wasu ‘yan takaran
  • Tsohon shugaban hafsun sojojin rurwa, Usman Oyibe Jibrin ya na cikin wadanda ake ganin za a gwabza da su

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Rahotonmu ya kawo bayanai game da wadanda ke kan gaba a zaben Gwamnan Kogi.

1. Ahmad Usman Ododo (APC)

• An haifi Ahmed Usman Ododo ne a shekarun 1960s, ana hasashen yanzu ya haura shekara 50.

• ‘Dan takaran na APC ya fito daga karamar hukumar Okene ne, saboda haka ya na cikin kabilar Ebira

Kara karanta wannan

Ana ta Surutu Yayin da Tinubu Ya Yi Nade-Naden Mukamai 5 a Kwana 1 Daga Saudi

• A jami’ar Ahmadu Bello a Zariya Ahmed Usman Ododo ya yi digiri a fannin akanta a shekarun baya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

• Da ya tashi yin digirgir a bangaren MBA, ‘dan takaran na APC a zaben 2023 ya tafi jami’ar Legas

• Ododo ya kware a fannin akanta da kula da kudi musamman gudanar da sha’anin kananan hukumomi

• Babban ‘dan siyasar ya rike babban mai binciken kudin kananan hukumomin jihar Kogi a baya

• Gwamna Yahaya Bello ya nada shi ya zama shugaban hukumar da ke tattara haraji a Kogi

• A tsawon aikin da ya yi, Ahmed Ododo ya na da rajista da kungiyoyin ICAN, ANAN da kuma IIA.

'Yan takaran Kogi
'Yan takaran Gwamnan Kogi Hoto: murtalaajaka.com.ng, kogistatehub.com
Asali: UGC

2. Dino Melaye (PDP)

• A ranar 7 ga watan Junairu, 1974 aka haifi Dino Melaye a garin Kano, daga baya ya koma Kogi.

• Asalinsa mutumin Ayetoro Gbede ne a karamar hukumar Ijumu, su ne mutanen yammacin Kogi.

Kara karanta wannan

Kwadayi Ya Jawo Mana: Jagora a PDP Ya Fadi Wadanda Su ka Yi Sanadiyyar Fadi Zabe

• Dino ya yi sakandare a makarantar Abdulaziz Attah Memorial College da ke garin Okene.

• A jami’ar ABU Zariya ne Dino Melaye ya samu shaidar digiri a 2000, ya karanci ilmin sanin wurare

• Tun a jami’a ya rungumi siyasa, har ta kai ya jagoranci kungiyar NANS da majalisar matasan Afrika.

• Olusegun Obasanjo ya jawo Melaye, ya shugabanci majalisar da ke bada shawara a kan harkokin matasa

• A karkashin jam’iyyar PDP ya zama ‘dan majalisar Kabba/Ijumu, amma ya koma APC a 2015.

• A jam’iyyar APC ne Dino Melaye ya zama Sanata, kafin zaben 2019, sai su ka sake dawowa PDP.

• Bayan an kai ruwa-rana a 2019 ne ya rasa kujerarsa a majalisa da kotu ta umarci a sake yin zabe.

3. Murtala Yakubu Ajaka (SDP)

• An haifi Hon. Murtala Yakubu Ajaka a ranar ga watan Fubrairu 1978

• ‘Dan siyasar mai shekara 45 ya fito daga cikin kabilar Igala da su ka fi yawa a tsakiyar Kogi.

Kara karanta wannan

Kogi: "Na tsallake rijiya da baya sau 30" Ɗan takarar Gwamna a arewa ya faɗi mutanen da aka kashe

• Muri ya fara firamare a makarantar mishan ta Roman Catholic Mission (RCM) a Ajaka a garin Igalamela/Odolu, daga baya ya karasa a garin Idah.

• A Barewa College da ke garin Zariya a jihar Kaduna ya yi sakandarensa.

• Bayan nan sai ya tafi jami’ar Abuja domin digirin BSc a ilmin halayyar ‘Dan Adam.

• Daga nan ne ya shiga siyaa, ya fara zama mataimakin sakataren jam’iyyar AC na reshen Abuja

• Ajaka ya na rike da mukami a matakin kasa sai aka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013.

• Sannu a hankali Murtala Yakubu Ajaka ya yi ta rike mukamai har zuwa mataimakin sakataren yada labarai.

4. Usman Oyibe Jibrin (Accord)

• Usman Oyibe Jibrin ya zo duniya ne a ranar 16 ga Satumban 1959 a wani kauye mai suna Okura Olafia

• Sojan ya tashi ne a karamar hukumar Dekina a jihar Kogi kafin ya tafi karatu a jihar Kaduna.

• A shekarar 1982 aka kaddamar da Usman Jibrin a matsayin soja bayan gama karatu a makarantar NDA.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

• Lokacin da aka yaye su daga gidan soja, shi ne ya zama na farko a sahun sojojin ruwa a shekarar.

• ‘Dan takaran na Accord ya yi aiki dabam-dabam a gidan soja, har ya rike makarantun sojojin.

• Zuwa shekarar 2011 ya zama babban jami’i a hedikwatar sojojin ruwa, daga nan ya yi aiki a Kamaru.

• A yayin da yake soja, ya taba zama shugaban sashen horaswa a hedikwatar tsaro da ke Abuja.

• A farkon 2014 ya gaji Vice Admiral Dele Joseph Ezeoba a matsayin Shugaban hafsun sojojin ruwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel