Zaben Jihohi: Abubawa 3 da Baku Sani Ba Game da Dan Takarar Jam’iyyar APC a Zaben

Zaben Jihohi: Abubawa 3 da Baku Sani Ba Game da Dan Takarar Jam’iyyar APC a Zaben

A yau Asabar ce 11 ga watan Nuwamba ake zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yenagoa, Bayelsa – Dan takarar gwamna a jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya na gaba-gaba a cikin ‘yan takarar zaben gwamna a jihar.

Abubuwa uku da baku sani ba game da dan takarar jam'iyyar APC, Sylva
Ana ci gaba da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi da Imo. Hoto: Timipre Sylva.
Asali: Twitter

A yau Asabar 11 ga watan Nuwamba ake zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi, Legit ta tattaro.

Duk da ya ke Sylva tsohon gwamna ne a jihar Bayelsa kuma ya rike mukamin Minsitan Man Fetur amma zai taka muhimmiyar rawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Yadda Sylva ya yi nasarar zama dan takarar APC

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Bayelsa: Jam’iyyar LP ta gamu da gagarumin matsala

Babbar kotun Tarayya da ke Abuja tun farko ta dakatar da Sylva daga takarar gwamnan jihar.

Daga bisani kotun daukaka kara ta ba shi damar tsayawa takara a zaben da ake gudanar wa a yau Asabar, cewar Vanguard.

Mai Sharia, Okorowo ya ce an rantsar da Sylva a matsayin gwamnan Bayelsa har sau biyu kuma ya mulki jihar na tsawon shekaru biyar.

Ya ce don haka babu dalilin da zai saka a sake rantsar da Sylva a matsayin gwamnan jihar a karo na uku.

Bayan hukuncin kotun ne hukumar zabe ta cire sunan Sylva daga jerin masu takara a zaben Bayelsa.

2. Mene zai iya bai wa Sylva nasara a zaben?

Sylva yana da magoya baya sosai a siyasa ganin cewa ya rike mukamin gwamnan jihar da kuma Minista a Najeriya, cewar Punch.

Sylva a baya ya taba alfahari da cewa:

“A yanzu haka ni tsohon gwamnan ne, don haka babu wani sabon abu a cikin wannan a wuri na.”

Kara karanta wannan

Dakarun soji sun damke wasu motoci 3 da ake zargi a zaben jihar Kogi

3. Me zai hana Sylva rashin nasara a zaben?

Sylva ka iya rasa kujerar gwamna saboda rikicin cikin gida na jam’iyyar APC sabanin takwarsa na PDP, Douye Diri da ke da goyon baya sosai.

Wasu daga cikin ‘yan jami’iyyar APC sun bayyana cewa kullum soyayyar Sylva kara disashewa ta ke yi a zuciyar ‘yan jihar.

Wannan bai rasa nasaba da yadda tsohon ministan ya rike jam’iyyar bayan samun nasara a zaben fidda gwani, cewar Premium Times.

Melayi ya yi wa ‘yan Kogi alkawari

Kun ji cewa, dan takarar jam’iyyar PDP a jihar Kogi Dino Melaye ya yi alkawarin gina Otal a saman ruwa.

Melaye ya bayyana haka ne a yayin kamfe inda ya ce hakan zai bunkasa tattalin arzikin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel