Gwamnonin PDP Sun Kira Taron Gaggawa a Kan Yunkurin Tsige Gwamnan Jihar Ribas

Gwamnonin PDP Sun Kira Taron Gaggawa a Kan Yunkurin Tsige Gwamnan Jihar Ribas

  • Kungiyar PDP-GF za ta yi zaman gaggawa a sanadiyyar rigimar siyasar da ta barke a jihar Ribas a makon nan
  • PDP-GF za ta yi kokarin goyon bayan Similaye Fubara a sabanin da ake tunani ya samu da Mista Nyesom Wike
  • Gwamna Seyi Makinde ya na cikin manyan Gwamnonin PDP, da shi aka kafa G5 a 2023 wanda Wike ya jagoranta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A sakamakon abubuwan da ke faruwa a jihar Ribas, gwamnonin da ke mulki a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP sun kira taro.

A rahoton da Tribune ta fitar, an fahimci cewa kungiyar gwamnonin PDP watau PDP-GF za ta yi wannan zama na musamman ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamna ya sa labule da manyan dattawan PDP da Sarakunan jiharsa, bayanai sun fito

Gwamnonin babban jam’iyyar adawar za su hadu a gidan gwamnan jihar Akwa Ibom da ke unguwar Asokoro domin tattauna rikicin siyasar.

Ribas
Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Ribas Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadan Similaye Fubara vs Nyesom Wike

Ana sa ran kungiyar gwamnonin ta duba sabanin da ake zargin an samu tsakanin takawaransu Similaye Fubara da kuma Nyesom Wike.

Da alamu babu jituwa yanzu tsakanin Gwamnan na Ribas da uban gidansa watau Nyesom Wike wanda yanzu Minista ne shi a gwamnatin APC.

PDP GF za ta taimaki Gwamnan Ribas

Jaridar ta ce duk da an zabi Fubara ne a karkashin jam’iyyar PDP, sabon Gwamnan bai saba shiga cikin harkokin da su ka shafi kungiyar ba.

An kafa kungiyar gwamnonin na PDP ne domin samun hadin-kai tsakanin ‘yan jam’iyya.

A yanzu da matsala ta taso, ana sa ran kungiyar gwamnonin za ta mara masa baya domin ganin ta hana ‘yan majalisa tunbuke shi daga mulki.

Kara karanta wannan

Dattijon Neja Delta ya fadi wanda Wike yake so ya kakaba ya zama gwamnan Ribas

Wike da G5 sun zama ala-ka-kai a PDP?

A lokacin da Nyesom Wike ya na gwamna, shi da wasu abokan aikinsa da su ka kira kan su G5, sun kawowa PDP cikas a zaben shugaban kasa.

Gwamnonin lokacin (har da Seyi Makinde) sun ki goyon bayan Atiku Abubakar a babban zabe, amma sun marawa PDP baya a zabukan gwamna.

Tun lokacin wasu su ka rika bada shawarar a hukunta Wike da ‘yan tafiyar G5 saboda juya bayan da su ka yi, jam’iyya ba ta iya yin hakan ba.

Clark: "Tinubu ya ja wa Wike kunne"

A baya an fahimci cewa idan mutanen Nyesom Wike sun samu yadda su ke so, za a tsige Simi Fubara daga mulki bayan wata biyar da shiga ofis.

Edwin Clark ya ce Shugaban majalisar dokoki, Rt. Hon. Martins Amaehwule ake so ya zama Gwamna, dattijon ya ce dole a ja kunnen Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel