Gwamnonin PDP Masu Rigima da Atiku Sun Fadawa Tinubu Abu 1 da Suke Bukata a Wajensa

Gwamnonin PDP Masu Rigima da Atiku Sun Fadawa Tinubu Abu 1 da Suke Bukata a Wajensa

  • Gwamnonin da suka shiga kungiyar G5 a jam’iyyar PDP sun jerowa Bola Tinubu abin da suke bukata
  • ‘Yan G5 za su marawa takarar Tinubu baya da sharadin zai goyi bayan sauran ‘yan takaran PDP a jihohinsu
  • Wadannan Gwamnoni su na rikici da Atiku Abubakar ne kurum, ba su isa suyi watsi da jam’iyyar PDP ba

London - Gwamnonin nan biyar da aka ja daga da su a jam’iyyar hamayya ta PDP sun bukaci goyon bayan ‘Dan takaran APC a 2023, Bola Tinubu a jihohinsu.

Rahoton Punch na ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba 2022, ya nuna Gwamnonin na PDP su na so Bola Tinubu ya goyi bayan ‘yan takaransu a zaben 2023.

Wannan shi ne bukatar da Gwamnonin suka gabatar lokacin da aka zauna. Bode George, Donald Duke, Jonah Jang, da Olusegun Mimiko sun halarci zaman.

Kara karanta wannan

Magoya Bayan Tinubu Sun Kinkimo Aiki, Sun Aika Sako ga Atiku, Kwankwaso da Peter Obi

Majiya mai karfi ta ce Gwamnonin su na hangen makomar siyasarsu, saboda haka su ke so Tinubu ya goyi bayan ‘yan takaran PDP a zaben Gwamna da majalisa.

Inda kurar 'Yan G5 ta ke a 2023

Alal misali, Wike bai neman takarar wata kujera, amma ya tsaida Siminalayi Fubara a matsayin ‘dan takarar Gwamna da masu takarar Sanata a inuwar PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Irinsu Gwamnan Benuwai, Abia da Enugu; Samuel Ortom, Victor Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi duk su na neman zama Sanataoci a karkashin PDP a zaben 2023.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da kusoshin APC a taro Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A gefe guda, Gwamna Seyi Makinde yana neman ya zarce domin yanzu yake wa’adin farko, sai ya yi hattara saboda APC za ta iya karbe kujerar da yake kai a badi.

Idan gwamnonin suka yi sakaci wajen goyon bayan jam’iyyar APC saboda adawar da suke yi wa Atiku Abubakar, babu mamaki su sha kashi a takarar da suke yi.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

Ba a cin ma matsaya ba tukuna

Jaridar ta ce a karshe ba a iya cin ma matsaya a wannan zama da aka yi a birnin Landan ba. Wata majiya ta ce bukatun gwamnonin sun yi wa APC mai-ci tsauri.

Kafin Bola Tinubu ya dauki matsaya, sai ya zauna da masu ba shi shawara da na-kusa da shi.

Tsoron da APC za ta ji idan ta goyi bayan G5 shi ne makomar ‘yan takaran da tsaida. jam’iyyar ta na sa ran Rabaren Hyacinth Alia zai lashe zaben jihar Benuwai.

Sai dai babu tabbacin jam’iyyar APC da ‘yan takaranta za su iya tabuka wani abin a kan PDP a sauran jihohin kamarsu Abia, Enugu da kuma Ribas a zaben badi.

Kalubale a gaban Tinubu

Ku na da labari cewa takarar da Asiwaju Bola Tinubu yake yi a inuwar Jam’iyyar APC mai-mulki tana fama da wasu kalubale tun daga cikin gida kafin a fita waje.

Kiristoci da-dama za su ki zaben APC saboda tikitin Musulmi-Musulmi da jam'iyyar ta fito da shi, sannan an yi watsi da wasu jiga-jigan APC wajen aikin kamfe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel