Wata Sabuwa a PDP: Tambuwal Bai Sauka Daga Kujerarsa ba, Yana nan – PDP GF

Wata Sabuwa a PDP: Tambuwal Bai Sauka Daga Kujerarsa ba, Yana nan – PDP GF

  • Shugaban kungiyar Peoples Democratic Party Governors Forum (PDP-GF) yace ba su samu canjin shugaba ba
  • C.I.D. Maduabum yace PDP GF ba ta san da maganar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi murabus ba
  • A jiya sanarwa ta fito cewa Gwamnan Sokoto ya sauka daga matayinsa, an zabi Gwamnan Oyo ya gaje shi

Abuja - Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal bai sauka daga kujerarsa ta shugaban gwamnonin PDP ba.

The Cable ta fitar da wannan rahoto a yammacin Alhamis, 8 ga watan Satumba 2022, bayan labari ya karade ko ina cewa har an nada Seyi Makinde.

A jawabin da Darekta Janar na kungiyar gwamnonin PDP, C.I.D. Maduabum ya fitar, yace Aminu Waziri Tambuwal bai bar kujerar da yake kai ba.

C.I.D. Maduabum yake cewa gwamnan na Sokoto zai cigaba da kokari wajen ganin an shawo kan matsalolin cikin gidan da suka bijirowa jam’iyyar

Kara karanta wannan

Karin bayani: An bayyana gwamnan da ya maye gurbin Tambuwal a shugabancin gwamnonin PDP

Tambuwal na nan - C.I.D. Maduabum

“Muna masu sanar da jama’a da sauran masu ruwa da tsaki a Peoples Democratic Party cewa shugaban kungiyar gwamnonin kungiyar Peoples Democratic Party Governors Forum (PDP-GF), Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal, CFR bai yi murabus ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akasin abin da wasu gidajen jaridu da suke yadawa."

- C.I.D. Maduabum

Tambuwal
Aminu Tambuwal da wasu Gwamnoni Hoto: @awtambuwal
Asali: Twitter

Vanguard tace jawabin ya kara da cewa kungiyar PDP GF za ta kira taro kwanan nan, kuma ana sa ran Aminu Tambuwal ne zai jagoranci wannan zama.

“Kungiyar gwamnonin PDP suna aiki ta bayan fage domin shawo kan duk wasu sabani da suka bijirowa jam’iyyar.”
A game da wannan, ba da dadewa ba kungiyar za ta kira zama.”

- C.I.D. Maduabum

Kujerar Shugaban PDP GF

Tambuwal ya karbi wannan mukami ne daga hannun Ayodele Fayose wanda ya sauka a 2018. Kafinsa Seriake Dickson ne ya jagoranci gwamnonin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Aminu Tambuwal Ya Yi Murabus Daga Kan Muƙaminsa Na PDP

Gwamnan na Sokoto ya kara da gwamnonin Taraba da Benuwai wajen karbar shugabancin kungiyar. Ana sa rai bayan shi, kujerar za ta bar Arewa.

Peter Obi zai bata mana lissafi - Ifeanyi Okowa

An ji ‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP, Ifeanyi Okowa yace sun yi fatan ina ma Peter Obi bai shiga takara ba domin zai jika masu aiki.

A yankin Kudu maso gabashin Najeriya, zaben 2023 zai kasance tsakanin PDP da LP ne, Dr. Ifeanyi Okowa yace ba a yin batun APC ko irinsu NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel