Oonin Ife: Sarkin Yarabawa Ya Bukaci ’Yarsa Ta Fito da Mijin Aure Tun da Girma Ya Zo

Oonin Ife: Sarkin Yarabawa Ya Bukaci ’Yarsa Ta Fito da Mijin Aure Tun da Girma Ya Zo

  • Babban sarkin Yarabawa, Oba Adeyeye Ogunwusi ya yi kira ga yarsa ta fitar da mijin aure a yau Litinin, 20 ga watan Mayu
  • Sarkin ya yi kiran ne ga yarsa gimbiya Adeola Adeyeye yayin da ta ke bikin murnar cika shekaru 30 da zuwan ta duniya
  • Sakon da sarkin ya wallafa ya ja hankulan masu amfani da kafafen sada zumunta musamman matasa wajen nuna son auren ta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Babba sarkin Yarabawa Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi ya bukaci 'yarsa mai suna Adeola Adeyeye ta fitar da mijin aure.

Sarkin Yarbawa
ooni na Ife ya yi kira ga 'yarsa kan ta fitar da miji lokacin murnar cika shekaru 30. Hoto: @deolzz, @ooniadimulaife (Instagram)
Asali: Twitter

Sarkin ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya aika mata lokacin bikin cikarta shekaru 30 da haihuwa.

Kara karanta wannan

Harin masallacin Kano ya haifar da marayu da Zawarawa da dama

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa sarkin ya turawa yar tashi sakon ne a yau Litinin, 20 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ranar Haihuwa: Sarki ya taya 'yarsa murna

Oba Adeyeye Ogunwusi ya taya yarsa murnar cika shekaru 30 a yau Litinin, 30 ga watan Mayu in da ya mata fatan alheri da kuma adduo'i.

Sarkin ya kuma nuna cewa lallai a yanzu diyar ta shi ta kai lokacin aure saboda haka sai ta fitar da miji.

Aure durin Sarkin Ife a kan Adeola

Ooni na Ife ya bayyana irin fatan da yake da shi a kan babbar 'yarsa, sarauniya Adeola cikin sakon da ya wallafa.

Ya ce a lokacin da ta ke shekaru 10 yana mata fatan samun ilimi da gobe mai kyau. Da ta kai shekaru 20 kuma ya mata fatan samun halaye na gari.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya yi martani kan matsalar da ya ke fuskanta daga haɗewar Atiku da Obi

Amma a yanzu da ta cika shekaru 30 ba abin da yake mata fata sai samun miji na gari domin yin aure, rahoton jaridar Tribune.

Mutane sun yi martani kan maganar sarkin

Sakon da sarkin ya tura ya ja hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta ta inda kowa ke tofa albarkacin baki.

Sai dai da yawa daga cikin matasa sun nuna sha'awar auren yar sarkin a cikin sakonnin da suka wallafa a kafar Instagram.

Sarkin Ife ya yi sabon aure

A wani rahoton, kun ji cewa watanni bayan rabuwarsa da tsohuwar matarsa, mai martaba Ooni na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi, ya yi sabuwar amarya.

Basaraken ya yi wuf da wata kyakkyawar budurwa mai suna Olori Mariam Anako a wani kasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel