Bara a Titi: Gwamnatin Kwara Ta Kwashe Almajirai 158, Ta Mayar da Su Jihohinsu

Bara a Titi: Gwamnatin Kwara Ta Kwashe Almajirai 158, Ta Mayar da Su Jihohinsu

  • Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana cewa, ta kwashe akalla almajirai 158 da ke bara a kan titunan Ilorin, babban birnin jihar
  • Kwamishiniyar cigaban al’umma ta jihar, Misis Afolashade Opeyemi ce ta bayyana wa 'yan jarida hakan a ranar Litinin
  • Misis Afolashade Opeyemi wadda ta ce an mayar da almajiran jihohin su na asali, ta kuma ce an kama wasu da makamai da layu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ilorin, jihar Kwara - Akalla almajirai 158 ne gwamnatin jihar Kwara ta kwashe daga titunan Ilorin tare da mayar da su jihohinsu a cikin shekara daya.

Gwamnatin Kwara ta dauki mataki kan almajirai da ke bara a Ilorin
Gwamnatin Kwara ta kwashe almajirai daga titin Ilorin. Hoto: @RealAARahman
Asali: Twitter

Kwamishiniyar cigaban al’umma ta jihar, Misis Afolashade Opeyemi ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

An kwashe almajirai 158 daga Kwara

Misis Opeyemi ta ce galibin alhamjiran da aka kwashe sun fito ne daga jihohin Bauchi da Kano da sauran jihohin Arewa, in ji rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishiniyar ta koka, ta ce almajiran sun haifar da matsalar zamantakewa a Ilorin saboda yawan barace-barace a titunan birnin.

“Mun kwashe almajira 158 daga kan tituna. An kai samame a karon farko inda aka kama 88 yayin da aka kara kama wasu 70 daga baya. Tuni aka mayar da su jihohin su na asali."

- A cewar Misis Opeyemi.

An kama almajirai da makamai

Opeyemi ta kara da cewa an gano makamai masu hadari kamar bindigu, wukake, laya da sauran mugayen makamai a hannun mabaratan da aka kwashe.

Ta yi mamakin abin da mabarata za u yi da laya da bindigogi, inda ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Sojoji sun ceto mutum 386 da 'yan Boko Haram suka sace tsawon shekaru 10

"Bincikenmu tabbaci ne kan cewa masu aikata laifuffuka suna ajiye bindigogi da sauran makamansu a hannun almajirai."

A watan Satumbar 2023, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin Kwara ta kwashe almajirai daga titunan Ilorin, babban birnin jihar.

Gobara ta tashi a makarantar Anambra

A wani labarin, mun ruwaito cewa gobara ta tashi a wata makarantar addini ta Bishop Crowther Memorial da ke Awka a jihar Anambra.

An ce dalibi daya ya mutu a gobarar da ta kama a tsakiyar daren ranar Asabar inda kuma ta lalata kayayakin da ke a dakin kwanan dalibai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel