Jigon PDP, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi Kan kin Bayyana Digiri Dinsa Ga INEC

Jigon PDP, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi Kan kin Bayyana Digiri Dinsa Ga INEC

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya sha suka bayan hira da gidan talabijin na Arise
  • Jigon jam'iyyar PDP, Reno Omokri ya caccaki Peter Obi kan shaidar takardun karatunsa bayan Atiku ya samu damar ganin takardun Tinubu
  • Omokri ya tambayi Obi dalillin kin mika takardar kammala digiri dinsa ga hukumar zabe ta INEC lokacin zaben shugaban kasa

FCT, Abuja - Jigo a jam'iyyar PDP, Reno Omokri ya yi martani ga dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi.

Omokri wanda tsohon hadimin shugaban kasa ne ya bukaci Peter Obi ya bayyana takardar shaidar kammala digiri dinsa, Legit ta tattaro.

Reno ya caccaki Peter Obi kan takardun Tinubu
Reno Omokri Ya Soki Peter Obi Kan Takardun Tinubu. Hoto: Bola Tinubu, Reno Omokri.
Asali: Facebook

Meye Reno ke cewa kan takardun Peter Obi?

Reno ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata 3 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Takardun Karatu: Yadda Atiku Yake Shirin Kawo Karshen Zaman Bola Tinubu a Aso Rock

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce me yasa Obi bai mika takardar shaidar kammala digiri dinsa ba na Jami'ar Najeriya ta Nsukka.

Wannan na zuwa ne yayin da Jami'ar Chicago ta turawa Atiku Abubakar wasu daga cikin takardun Bola Tinubu bayan ya bukaci hakan.

Yadda Omokri ya soki Peter Obi kan takardun Tinubu

Yayin da ya ke caccakar hirar da Obi ya yi, Omokri ya ce:

"Peter Obi, Jami'ar Chicago ta tabbatar da takardar shaidar karatun Tinubu da kuma ingancinsu, sai jiya da safe ka ke hira da gidan talabijin na Arise kan cewa takardun Tinubu jabu ne.
"Yanzu ka amsa wannan tambaya, me yasa ba ka mika takardar shaidar kammala digiri din ka ba ga hukumar zabe ta INEC?

Wannan martani na Omokri na zuwa ne bayan Atiku Abubakar ya samu shaidar takardun karatun Shugaba Bola Tinubu daga Jami'ar Chicago da ke Amurka.

Kara karanta wannan

Atiku Zai Sheka Kotun Koli da Karfinsa, Jami’ar Amurka Ta Mallaka Masa Takardun Tinubu

Atiku Abubakar na kalubalantar zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a jam'iyyar APC.

Atiku ya samo takardun karatun Tinubu

A wani labarin, Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya lalubo takardun karatun Tinubu.

Atiku ya shigar da kara kan zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Faburairu na wannan shekara.

A watan Satumba ne kotun sauraran kararrakin zaben shugaban kasa ta tabbatar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel