Kai Tsaye: Yadda Kotu Ke Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

Kai Tsaye: Yadda Kotu Ke Yanke Hukunci Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna

A yau Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023, Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna za ta yanke hukunci kan zaben.

Jam'iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Mohammed Isah Ashiru, ne suka shigar da kara a gaban kotun suna kalubalantar nasarar Uba Sani na jam'iyyar APC.

Kotun zaben za ta sanar da hukunci ne ta manhajar Zoom.

Tuni aka kafa majigi da kyamarori a kotun, inda daga bisani alkalai suka bayyana ta manhajar Zoom, suka fara sanar da matsayar kotu.

Kotu ta tabbatar da nasarar Malam Uba Sani

Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben gwamna ta tabbatar da sahihancin nasarar gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kotun ta tabbatar da nasarar APC ne yayin da take yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP, da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan, suka shigar gabanta.

PDP da Isa Ashiru sun shigar da ƙara suna mai ƙalubalantar sakamAkon zaben gwamnan Kaduna, amma Kotu ta ce Malam Sani ne sahihin wanda ya ci zaɓe.

Tun a wancan lokaci, hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta ayyana Sanata Uba Sani na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris da ƙuri'a mafi rinjaye.

Amma Ashiru da jam’iyyarsa ta PDP suka ƙi amincewa da sakamakon da INEC ta bayyana, inda suka garzaya Kotu suka shigar da ƙara.

Kwamitin alƙalai uku karkashin jagorancin mai shari'a Victor Oviawe ya yanke hukunci ta hanyar manhajar Zoom ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023.

Kotu ta yi watsi da shaidun PDP 6

Kotun zaɓe ta yi watsi da shaidar Ɗanjuma Sarki (wakilin PDP a zabe) da ƙarin wasu shaidu 5 waɗanda jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru suka gabatar.

Haka nan kuma Kotun ta ce masu shigar da ƙara sun gaza gamsar da ita kan zargin maguɗin zaɓe a ƙaramar hukumar Lere da ke jihar Kaduna.

Kotu ta kori buƙatar gwamna Uba Sani ta 2

Kotun zaɓe ta ƙara fatali da buƙata ta 2 da Uba Sani da APC suka shigar suna buƙatar a kori karar jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Isa Ashiru Kudan.

Gwamnan da jam'iyyarsa ta APC sun kafa hujjar cewa masu shigar da ƙara sun riga sun yi watsi da ƙarar, bisa haka suka buƙaci Kotu ta kori ƙarar gaba ɗaya.

Amma a zaman yanke hukuncin da ke gudana yau Alhamis, Kotun ta yi fatali wannan buƙata ta biyu da waɗanda ake ƙara suka shigar, The Nation ta rahoto.

Kotu ta yi watsi da bukatar Gwamna Uba Sani kan karar PDP da Ashiru

Yayin da kotun zaben ta fara yanke hukunci, ta yi watsi da karar farko da Gwamna Uba Sani ya shigar a kan PDP da dan takararta, Isah Mohammed Ashiru.

Gwamna Sani ya nemi kotu ta kori karar da PDP ta shigar kan hujjar cewa an shigar da ita ne bayan kwana 21 da doka ta yarda da shi.

Sai dai kuma kotun ta ce an shigar da karar ne a ranar 10 ga watan Afrilun 2023, saboda haka ta yi watsi da bukatar gwamnan, rahoton The Nation.

An tsaurara matakan tsaro

Tuni aka tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na jihar don gudun samun tashe-tashen hankula bayan sanar da hukuncin kotun, sashin Hausa na BBC ya rahoto.

Tun bayan fara sauraron karar a watan Yuni, dandazon magoya bayan jam'iyyun sukan yi dafifi zuwa kotun domin gani da sauraron yadda karar ke gudana.

A yayin zaman kotun ana ta tayar da jijiyar wuya tsakanin lauyoyin bangarorin biyu inda kowa ke kokarin tabbatar da hujjojinsa.

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262