Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Ɗan Majalisar PDP a Jihar Filato, Ta Baiwa APC

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Ɗan Majalisar PDP a Jihar Filato, Ta Baiwa APC

  • Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaben 'yan majalisar jiha da na tarayya ta ƙara soke nasarar ɗan majalisar PDP a jihar Filato
  • Yayin yanke hukunci ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, Kotun ta ce PDP ba ta da sahihin tsarin tsaida 'yan takara a lokacin zaɓen da ya gabata
  • A cewar shugaban kwamitin alƙalan Kotun, PDP ta yi kunnen uwar shegu da umarnin babbar Kotun jihar Filato na shirya sabon taro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Plateau - Kotun saurararon ƙorafe-ƙorafen zaben 'yan majalisar jiha da na tarayya ta soke nasarar ɗan majalisar jihar Filato, Timothy Dantong, na jam'iyyar PDP.

Bayan haka Kotun ta ayyana Moses Dachum na jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen mamba mai wakiltar mazaɓar Riyom a majalisar dokokin jihar Filato.

Kotun ta soke nasarar dan majalisar PDP a Filato.
Kotun Zabe Ta Kwace Kujerar Ɗan Majalisar PDP a Jihar Filato, Ta Baiwa APC Hoto: Thenation
Asali: UGC

Kwamitin alkalan kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a B.M Tukur ne ya yanke wannan hukunci ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Yi Nasara, Kotun Zaɓe Ta Yanke Hukuncin Kan Nasarar Wani Gwamna

Me ya sa Kotu ta soke nasarar ɗan majalisar na PDP

Kotun ta bayyana cewa jam'iyyar PDP ba ta da ingantaccen tsarin da zai ba ta damar tsaida 'yan takara a lokacin da aka yi zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ta faru ne sakamakon ƙin bin umarnin mai shari'a S P Gang na Kotun jihar Filato, wanda ya yanke hukuncin cewa PDP ta sake gangamin taro ranar 26 ga watan Nuwamba, 2020.

Bisa haka Alƙalan Kotun suka yanke hukuncin tsige ɗan majalisar PDP da INEC ta bayyana, kana suka ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya ci zaɓe na ainihi.

Wannan ba shi ne karo na farko da Kotun zabe ta rushe nasarar jam'iyyar PDP kan wannan dalili na ƙin bin umarnin Kotu ba a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya, Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Bamu Yarda Ba" Jam'iyyar PDP Ta Fusata Bayan Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan APC

Sai dai abin mamakin, Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Celeb Mutfwanga na PDP a jihar Filato, inda ta ce PDP ta sake gudanar da gangamin taron kamar yadda Kotu ta umarta.

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamna Uno Na Akwa Ibom

A wani rahoton na daban Kotun zaɓe mai zama a Uyo ta tabbatar da nasarar Gwamna Umo Eno a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar Akwa Ibom.

Kotun ta yi fatali da ƙarar jam'iyyar ADC da ɗan takararta, Ezekiel Nyaetok, waɗanda suka.ƙalubalancin nasarar Gwamna Eno na PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel