Jerin Sunayen Gwamnonin PDP Da Suka Yi Nasara a kotun Zabe

Jerin Sunayen Gwamnonin PDP Da Suka Yi Nasara a kotun Zabe

Kotunan sauraron ƙararrakin zaɓukan gwamnoni a Najeriya, na cigaba da zartar hukuncinsu kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarorin da wasu gwamnoni suka samu a zaɓen 2023.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yayin da wasu gwamnonin suka samu nasara a kotun, wasu kuma sun rasa kujerunsu bayan hukuncin kotun.

Gwamnonin PDP da suka samu nasara a kotu
Jerin gwamnonin PDP da suka samu nasara a kotun zabe Hoto: Peter Ndubuisi Mbah, Senator Bala Abdulkadir Mohammed, Governor Dauda Lawal
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro jerin sunayen gwamnonin da aka zaba a ƙarƙashin jam'iyyar PDP da suka yi nasara a kotun:

1. Bala Mohammed (Gwamnan Bauchi)

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed
Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin jagorancin mai shari’a P.T Kwahar a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba ta tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed.

Kotun ta bayyana Gwamna Bala a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Bauchi na ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Cikin Gwamnan APC Ya Kada, Kotu Ta Bayyana Ranar Yanke Hukunci Kan Karar Da Ke Kalubalantar Nasararsa a Zabe

2. Peter Mbah (Gwamnan Enugu)

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Peter Mbah
Peter Mbah ya yi nasara a kotun zabe Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Asali: Facebook

An tabbatar da Peter Mbah a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Enugu.

Kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan jihar Enugu a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, ta yi watsi da dukkanin ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar gwamna Chijioke Edeogu na jam’iyyar Labour Party (LP) ya shigar yana kalubalantar nasarar Mbah a zaɓen.

3. Caleb Mutfwang (Gwamnan Plateau)

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Caleb Mutfwang
Kotu ta bayyyana Caleb Mutfwang a matsayin halastaccen gwamnan jihar Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Kotun zaɓe ta kori ƙarar da ke kalubalantar nasarar Gwamna Caleb Mutfwang, wacce ɗan takarar jam'iyyar APC Nentawe Yilwatda, ya shigar.

Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamna da ke zamanta a Jos babban birnin jihar Plateau, a ranar Juma’a, 22 ga watan Satumba, ta tabbatar da nasarar gwamna Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP.

Mai shari’a Sunday Olorundahunsi, da ke karanta hukuncin a ranar Juma’a, ya yi watsi da dukkanin ƙorafe-ƙorafen da ɗan takarar jam'iyyar APC.

4. Dauda Lawal (Gwamnan Zamfara)

Kotu ta tabbatar da nasarar gwamna Dauda Lawal
Kotu ta tabbatar da sahihancin zaben gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Zamfara ta tabbatar da nasarar gwamna Dauda Lawal a zaɓen ranar Litinin, 18 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP a Arewa

Kotun ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna Bello Matawalle suka shigar inda suke ƙalubalantar ayyana gwamna Lawal na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotu Za Ta Yi Hukunci Kan Zaben Gwamnan Legas

A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas ta shirya yanke hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar.

Kotun ta sanya ranar Litinin, 25 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta zartar da hukuncinta kan shari'ar da ke ƙaƙubalantar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel