Kwamishina A Kano Ya Yi Barazanar Kisa Ga Alkalan Kotun Zabe Kan Cin Hanci

Kwamishina A Kano Ya Yi Barazanar Kisa Ga Alkalan Kotun Zabe Kan Cin Hanci

  • Kwamishinan Safiyo a jihar Kano, Adamu Aliyu ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun zabe a jihar
  • Aliyu ya ce duk alkalin da ya karbi cin hanci da kuma sauya shari'a to ya zabi rayuwarsa ko kudin da ya karba
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben gwamna na watan Maris

Jihar Kano - Yayin da ake dakon hukuncin kotun zabe, kwamishinan Safiyo a jihar Kano, Adamu Aliyu ya yi barazana ga alkalan kotun.

Adamu ya yi wannan barazana ce a jiya Alhamis 14 ga watan Satumba, Legit ta tattaro.

Kwamishina a Kano ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun zabe
Kwamishina A Kano Ya Yi Barazanar Kisa Ga Alkalan Kotu. Hoto: Sabo Yusuf Chelsea.
Asali: Facebook

Meye kwamishinan ya ce a kan zaben Kano?

Ya ce duk wanda bai yi abin da ya dace ba zai iya rasa ransa in dai a kan gwamnatin Abba Kabir ne.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Koka, Ya Ce 'Yan Bindiga Sun Mamaye Jiharsa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi alkawarin kawo tarzoma da tashin hankali fiye da wanda 'yan jihohin Katsina da Zamfara da Kaduna ke ciki.

Kwamishinan na zargin alkalan kotun sun karbi cin hanci inda ya ce duk wanda ya aikata musu ba dai-dai ba zai iya rasa rayuwarsa.

Jam'iyya APC na kalubalantar zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris da cewa akwai matsaloli a ciki.

A ina kwamishinan ya yi wannan magana a Kano?

Aliyu ya yi wannan barazanar ce a dandazon taron 'yan jam'iyyar NNPP a jiya a Kano, Premium Times ta tattaro.

Taron wanda kuma an yi shi ne don yin addu'o'in samun nasara ga Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP.

Ya ce:

"Ina mika sako duk wani alkali da ya karbi cin hanci kuma ya yi hukunci ba dai-dai ba, to ya zabi rayuwarsa ko kudin da ya karba.

Kara karanta wannan

Ana Binciko Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7 a CBN

"Mun yi muku alkawari, kuma mun samu korafin ku, kuri'unku ba za su tafi a banza ba, sai dai mu rasa ranmu ko Kano ta tarwatse."

Ya ce kuna ganin halin da 'yan Zamfara da Kaduna da Katsina ke ciki, na rantse a kan kujerar nan sai masifar da Kano za ta shiga ta fi haka.

"Masifar da za ta faru a Kano a kan kujerar nan sai ta fi ta wadannan jihohi da kuma Borno."

NNPP TGabatar Da Sallah Don Neman Nasara Ga Abba Kabir

A wani labarin, magoya bayan jam'iyya mai mulki ta NNPP a jihar Kano sun gabatar da addu'o'i don samun nasara a kotu.

Jam'iyyar adawa ta APC ta shigar da kara kan tafka magudin zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel