Wole Soyinka Ya Tonawa Obidient Asiri, Ya Ce Sun San Peter Obi Bai Ci Zabe ba

Wole Soyinka Ya Tonawa Obidient Asiri, Ya Ce Sun San Peter Obi Bai Ci Zabe ba

  • Wole Soyinka bai da ra’ayin cewa Jam’iyyar LP ta lashe zaben shugaban kasa a maimakon APC
  • Ganin yadda LP ta gwabza da PDP da APC, Farfesan ya ce Peter Obi ya yi abin jinjina a 2023
  • Soyinka ya zargi kusoshin tafiyar LP da yaudarar matasa da zanga-zanga a kan magudin zabe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

South Africa - Shahararren Farfesan nan, Wole Soyinka, ya ce shugabannin jam’iyyar Labour Party (LP) sun san gaskiyar babban zaben da aka yi a bana.

A wajen wani taro da aka yi a birnin Stellenbosch, a Afrika ta Kudu, The Cable ta rahoto Farfesa Wole Soyinka ya na bayani game da siyasar Najeriya.

Masanin ingilishin ya zargi jagororin adawa na LP da yi wa ‘yan Najeriya musamman matasan da ke goyon bayan Peter Obi karya a kan zabe.

Kara karanta wannan

Mu ba Sakarkaru ba ne: Abin da Ya sa Wike Ya Dage Sai Ya Karya PDP - Mutumin Atiku

Peter Obi
'Dan takaran LP, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Peter Obi bai ci zaben 2023 ba

Obi da jam’iyyarsa ta LP ba ta gamsu da sakamakon zaben Fabrairu ba, su na ikirarin su ne ainihin wadanda su ka lashe takarar shugaban kasar Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ra’ayin masanin, ba haka abin yake ba, kuma ya ce jagororin jam’iyyar LP sun san da wannan. Jaridar Punch ta kawo wannan rahoto a ranar Laraba.

Raddi ga LP da Baba Ahmed

An bukaci Soyinka ya maida martani a kan kalaman da su ka fito daga bakin Yusuf Datti Baba-Ahmed bayan INEC ta ba jam’iyyar APC mai-ci nasara.

An rahoto Soyinka ya na mai cewa kowa ya san gaskiyar abin da ya faru a zaben, ya kuma ce mutane da-dama su na kaucewa gaskiyar lamarin ne.

A zaben shugaban kasar da ya gabata, Soyinka ya ce LP ta karbe tafiyar ‘yan kwandago, ya ce a karshe Peter Obi ya yi abin yabawa a siyasa.

Kara karanta wannan

Ga ci ga rashi: An kwace kujerar sanatan PDP a Arewa, an ba wani fitaccen tsohon gwamnan APC

Soyinka ya ce Obi ya yi kokari

Maimakon su rungumi matsayinsu na zama na uku, Soyinka ya ce sai LP ta zuga matasa su ka shiga zanga-zangar da za ta iya jawo mai-man 2011.

Farfesan ya tabo batun zabukan da aka yi a shekarun baya, ya tofa albarkacin bakinsa kan zaben shiyyoyi da aka yi a 1965, wanda ya jawo hayaniya.

A lokacin da ya je gidan rediyo a Ibadan a 1965, Soyinka ya ce ya na dauke da hujjoji kan zaben.

LP ta ce ta doke APC da PDP

Datti Baba-Ahmed wanda ya nemi takarar mataimakin shugaban kasa ya hakikance a kan LP ya kamata a ba nasara duk da jam’iyyarsa ta zo ta uku ne.

Tun a watan Maris tsohon Sanatan ya ce za su nemi hakkinsu a kotu, a lokacin ya bukaci magoya bayansu su fita a gwabza a zaben gwamna da jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel