Ya Kamata Maza Su Duba Yiwuwar Komawa Gefe Su Bar Wa Mata Siyasa, Akpabio

Ya Kamata Maza Su Duba Yiwuwar Komawa Gefe Su Bar Wa Mata Siyasa, Akpabio

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce akwai bukatar mata su rike madafun iko
  • Ya ce ya kamata maza su riƙa komawa gefe domin bai wa mata damar ɗarewa kujerun siyasa
  • Ya bayyana cewa adadin mata da ake da su a kujerun shugabanci ya yi kaɗan a halin da ake ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya ce yana dakyau a wasu lokutan maza su riƙa bai wa mata jan ragamar siyasar ƙasar nan.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, a wajen wani taro na ƙasa da ƙasa kan rawar da mata ke takawa a shugabanci.

Cibiyar Nazarin Dokoki da Dimokuradiyya ta ƙasa (NILDS) ce ta shirya taron kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wata Kungiya Ta Bukaci Ministocin Tinubu Su Yi Murabus, Ta Bayyana Dalilanta

Akpabio ya bukaci maza su bai wa mata damar hawa kujerun siyasa
Akpabio ya ce yana da kyau maza su duba yiwuwar bai wa mata damar ɗarewa kujerun siyasa. Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akpabio ya ce akwai bukatar mata a siyasa

Akpabio ya bayyana cewa yana matuƙar sha'awar ganin mata riƙe da kujerun shugabanci na siyasa a Najeriya.

Sai dai yanayin siyasar da ake ciki a yanzu, ba su cika samun kujerun shugabancin ba sai dai a ba su muƙamai a gwamnati.

Shugaban ya ce adadin matan da yanzu haka ke a Majalisar Dattawan Najeriya sun yi kaɗan, inda yake ganin ya kyautu a ce sun wuce hakan.

Ya ƙara da cewa a bisa wannan dalilin ne yake ganin ya kamata maza su riƙa komawa gefe a wasu lokutan domin bai wa mata damar samun kujerun siyasa.

Akpabio ya nemi a yaƙi wariyar jinsi

Akpabio ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar a yaƙi wariyar jinsin da ake nunawa mata a cikin al'umma musamman yayin neman shugabanci.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Hango Wani Sabon Abu Da Zai Faru a Mulkin Shugaba Tinubu

Ya ce wannan wani abu ne da Cibiyar Nazarin Dokokin ya kamata ta yi da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyin na kare haƙƙin mata kamar yadda The Punch ta wallafa.

Ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar a sauya yadda al'amura ke tafiya tun a baya da kuma yadda suke a yanzu, ta hanyar ƙarfafawa mata gwiwar su shiga siyasa.

Mata sun buƙaci Tinubu ya ba su damar gyara matatun man Najeriya

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan roƙon da ƙungiyar Injiniyoyi mata ta Najeriya (APWEN), ta yi ga Shugaba Tinubu da ya ba su damar gyara matatun man da ake da su.

Shugabar kungiyar, Atinuke Owolabi ce ta miƙa wannan buƙata ga shugaban ƙasar a wajen wata lakca a birnin Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel