Sunayen Mata da Buhari ya ba kujerar Minista a Gwamnatinsa a 2019
A yau, Talata, 23 ga Watan Yuli, 2019, shugaban kasar Najeriya ya aikawa majalisar dattawa jeringiyar wadanda ya ke so a tantance masa a matsayin sabbabin Ministoci na gwamnatin tarayya.
Kamar yadda mu ka fahimta a jeringiyar, daga cikin wannan mukamai fiye da 40 da shugaban kasar ya raba, mata sun samu kashi 16.3% a sabon gwamnatin APC ta shugaba Muhammadu Buhari.
Ga dai matan da su ka samu damar shiga cikin wannan jerin sababbin Ministoci:
1. Zainab Ahmed (Kaduna)
Shamsuna Ahmad ita ce tsohuwar Ministar kudi a gwamnatin da ta shude. Kafin nan ta rike karamar Ministar kasafi da tsare-tsare a farkon gwamnatin. Ta rike mukami a kuma lokacin PDP.
2. Paulen Talen (Filato)
Madam Paulen Talen ta na cikin wadanda a ke sa ran ta zama Minista bayan ta yi watsi da kujerar Jakadanci a mulkin Buhari. Tsohuwar mataimakiyar gwamnan ta rike Minista a lokacin Obasanjo.
3. Sharon Ikeazor (Anambra)
Ikeazor Sharon ce shugabar hukumar Pension Transitional Arrangement Directorate (PTAD) mai kula da fansho. Misis Sharon ta na cikin Ministoci biyu da a ka zakulo daga jihar Anambra.
KU KARANTA: PDP ta yi tir da sababbin Ministocin da Buhari ya nada
4. Ambasada Maryam Katagun (Bauchi)
Maryam Katagum ce Wakiliyar da Najeriya ta aika zuwa Majalisar UNESO. Katagum ta yi karatu ne a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da kuma wasu manyan makarantu da ke Landan a Ingila.
5. Ramatu Tijjani (Kogi)
Kwanan nan Ramatu Tijjani ta sauka daga kujerar shugaban mata na jam’iyyar APC na kasa. Tijanni babbar ‘yar siyasa ce da ta yi fice wanda ta fito daga Jihar Kogi tsakiyar Najeriya.
6. Gbemisola Saraki (Kwara)
Gbemi Saraki fitacciyar ‘yar siyasa ce kuma ‘yar gidan siyasa. Saraki ta rike kujera a majalisar wakilai da dattawa a yankin tsakiyar jihar Kwara. Gbemisola ‘yaruwar Bukola Saraki ce.
7. Sadiya Umar Faruk (Zamfara)
Mace ta karshe a wannan jeri ita ce Hajiya Sadiya Faruk wanda ta ke shugabantan hukumar NCFRMI mai kula da masu gudun hijira da wadanda ke fake a sansanin IDP a fadin Najeriya.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng