Rikicin PDP: Babban Jigo Ya Maka Mukaddashin Shugaban Jam'iyya a Gaban Kotu

Rikicin PDP: Babban Jigo Ya Maka Mukaddashin Shugaban Jam'iyya a Gaban Kotu

  • Rigingimun cikin gida da suka yi wa jam'iyyar PDP katutu sun sake buɗe sabon shafi kan batun shugaban jam'iyya na ƙasa
  • Wani babban jigo, Daboikiabo Warmate, ya maka muƙaddashin shugaban PDP, Umar Damagun, NWC da NEC a Kotu
  • Ya roƙi Kotu ta umarci NEC ta shirya taro cikin mako ɗaya domin maye gurbin manyan muƙamai na kasa da ba bu kowa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Babban jigo a jam'iyyar PDP, Daboikiabo Warmate, ya maka muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagun a gaban Kotu, The Cable ta ruwaito.

Mista Warmate, wanda ke jagorantar ƙungiyar masu kishin PDP (CPDPL) ya kuma kai ƙarar kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da kuma kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC).

An kai ƙarar shugaban PDP na riko, Umar Damagun.
Rikicin PDP: Babban Jigo Ya Maka Mukaddashin Shugaban Jam'iyya a Gaban Kotu Hoto: PDP
Asali: UGC

Meyasa jigon ya kai ƙara Kotu?

Warmate ya yi zargin cewa muƙaddashin shugaban PDP, NWC da kuma NEC, "Sun shure sashi na sashi na 31 sakin layi na huɗu na kundin tsarin mulkin PDP 2017 da aka yi wa garambawul."

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Babban Malamin Addini Ya Fadi Wani Mummunan Abu Da Zai Faru a Najeriya a Mulkin Tinubu, Ya Fadi Mafita

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon babbar jam'iyyar adawan ya kuma nuna cewa ginshiƙan PDP 3 da yake ƙara sun ƙi mutunta wanda tanadin doka da aka kafa jam'iyyar a kai da gangan.

A cewarsa, sashin ya tanadi cewa, "Ya kamata NEC ta shirya taro aƙalla sau ɗaya duk wata uku kan shugabancin PDP ko kuma idan kaso 2 cikin 3 na mambobin jam'iyya sun buƙaci haka."

"Kuma za a sanar da shugaban jam'iyya aƙalla kwana Bakwai gabanin ranar taron. Haka zalika mai yuwuwa shugaban jam'iyya ya kira taron gaggawa idan wata buƙata ta taso."

Ya ce ba bu wani taro da aka gudanar tun taron kwamitin NEC-PDP karo na 97 wanda ya gudana ranar 8 ga watan Satumba, 2022, kamar yadda Ripples ta rahoto.

Buƙatun da Jigon ya nema a Kotu

Bayan haka, Mista Warmate ya roƙi Kotu ta bada umarnin dakatar da waɗanda yake ƙara daga ci gaba da gudanar da harkokin jam'iyyar PDP nan gaba.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Bugu da ƙari, ya roƙi Kotu ta umarci NEC ta shirya taro cikin kwanaki 7 domin cike gurbin shugaban jam'iyya na ƙasa, Sakatare da wasu muƙamai da ba bu kowa a yanzu.

Ya kuma buƙaci kotun ta ci tarar waɗanda yake ƙara kudi naira miliyan 5 a matsayin kuɗin wahalhalun wannan shari'a.

Kotun Zabe Ta Tanadi hukuncinta Kan Shari'ar Gwamnan Kano

A wani rahoton kuma Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kano ta tanadi hukuncinta a kan ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar, gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar ne bayan jam'iyyun APC da NNPP sun kammala bayanansu na ƙarshe a zaman sauraron ƙarar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel