Peter Obi Ya Yi Magana Kan Batun Hadewa Da Atiku Da Kwankwaso Domin Kwace Mulki a Hannun APC

Peter Obi Ya Yi Magana Kan Batun Hadewa Da Atiku Da Kwankwaso Domin Kwace Mulki a Hannun APC

  • Peter Obi jagoran jam'iyyar Labour Party (LP), ya yi tsokaci kan batun cewa yana shirin haɗewa da Atiku da Kwankwaso
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023 ya bayyana cewa mafi yawan rahotannin da ke yawo kan batun jita-jita ce kawai
  • Peter Obi ya tabbatar da cewa yana nan zai cigaba da zama daram a jam'iyyar LP domin ƙara mata ƙarfi

Jihar Edo - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan rahotannin cewa zai yi haɗaka da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso, domin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC.

Peter Obi wanda ya yi martani a jihar Edo a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, ya tabbatarwa da magoya bayansa cewa yana tare da jam'iyyar LP, cewar rahoton Channels Tv.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Peter Obi ya magantu kan batun hadewa da Atiku da Kwankwaso
Peter Obi ya yi magana kan batun dunkulewar PDP, LP da NNPP Hoto: Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Babu batun hadewa da Atiku da Kwankwaso, Peter Obi

Da yake magana a wajen wani gangamin taron yaƙin neman zaɓe a jihar Edo, domin zaɓen ƙananan hukumomin jihar, Peter Obi, ya bayyana cewa wasu daga cikin abubuwan da su ke ji, jita-jita ce kawai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Labour Party za ta cigaba da ƙara haɓɓaka. Za mu cigaba da ƙara yin ƙarfi. Rabin abin da ku ke ji, jita-jita ce kawai, kada ku saurare su. A shirye mu ke wajen samar da sabuwar Najeriya inda za mu tashi daga masu ci zuwa masu samarwa."

Rahoton dunƙulewar jam'iyyun uku a waje ɗaya na zuwa ne ƙasa da watanni shida bayan zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairun 2023, inda Obi ya zo na uku a bayan Atiku Abubakar da Bola Tinubu wanda ya lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe: Babban Malamin Addini Shawarci 'Yan Najeriya Kan Abin Da Za Su Yi Idan Kotun Koli Ta Yi Hukunci

Rahotanni sun fito a ranar Litinin cewa Atiku, Obi da Kwankwaso na tattaunawa domin duba yiwuwar dunƙulewa waje ɗaya domin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar APC a shekarar 2027, idan har kotu ta ba jam'iyyar nasara a ƙarar da suka shigar gaban kotu.

Rahoton ya yi iƙirarin cewa shugabannin uku sun yanke shawarar su tsaya su zura ido su ga yadda hukuncin kotun zai kaya, kafin su ɗauki mataki na gaba.

Fintiri Ya Taya Wike Murna

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya taya tsohon gwamnan jihar Rivers murnar zama minista.

Gwamna Fintiri ya bayyana cewa Wike ya cancanci samun muƙamin da Shugaba Tinubu ya ba shi, inda ya nuna fatan cewa tsohon gwamnan zai yi abinda ya dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel