PDP Ta Saka Sunan Wike A Kwamitin Kamfe Na Jam'iyyar A Zaben Bayelsa Bayan Tantance Shi Ministan Tinubu

PDP Ta Saka Sunan Wike A Kwamitin Kamfe Na Jam'iyyar A Zaben Bayelsa Bayan Tantance Shi Ministan Tinubu

  • Wani abin mamaki ya faru yayin da jam'iyyar PDP ta saka sunan Nyesom Wike a kwamitin kamfe na zaben jihar Bayelsa
  • Shugaba Tinubu ya zabi Wike a matsayin wanda zai kasance minista a gwamnatinsa duk da kasancewar shi dan PDP
  • Jam'iyyar PDP a makon da ya gabata ta ce za ta dauki mataki a kan tsohon gwamnan bayan nada shi mukamin minista

Jihar Bayelsa - Jam'iyyar PDP ta saka sunan Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike a cikin kwamitin kamfe na jam'iyyar a zaben da za a yi a jihar Bayelsa.

Jam'iyyar ta kuma saka sunayen gwamnoni guda hudu da suka yi wa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Atiku Abubakar tawaye a zabe, Legit.ng ta tattaro.

Wike ya fito a kwamitin zabe a Bayelsa bayan tantance shi ministan Tinubu
An Tantance Wike A Matsayin Minista Kafin Jam'iyyar PDP Ta Saka Shi A Kwamitin Kamfe A Zaben Bayelsa. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Sakataren hulda da jama'a na jam'iyyar, Debo Olugunagba shi ya bayyana haka a ranar Litinin 31 ga watan Yuli da dare, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sabon Gwamna Zai Raba Buhuna 36, 000 na Kayan Abinci Kyauta a Kowane Gari

Gwamnonin G5 da suka fito a kwamitin yakin neman zaben Bayelsa

Sauran gwamnonin sun hada da gwamnan Oyo, Seyi Makinde da tsohon gwamnan Benue, Samuel Ortom da na Abia, Ikpeazu Okezie da kuma tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TheCable ta tattaro cewa Wike da Makinde da kuma Ipkeazu na cikin kwamitin kamfen na jihar Bayelsa yayin da Ortom ya samu fitowa a kwamitin a jihohin Kogi da Bayelsa.

Tsohon gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi kuma ya fito a kwamitin kamfe na jihohin Bayelsa da Imo.

Sanarwar PDP na saka sunan Wike a kwamitin zabe

A cewar sanarwar:

"Kwamitin masu ruwa da tsaki na PDP ta amince da zabar wadannan jiga-jigan a kwamitin kamfe na jihohin Bayelsa da Imo da Kogi a zaben da ke karatowa.
"Za a kaddamar da kwamitin a ranar Laraba 2 ga watan Agusta."

Kara karanta wannan

Kwamiti Ya Karbo Motoci 48 Daga Hannun Tsohon Gwamnan PDP da Mukarrabansa

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Shugaba Tinubu ya nada Wike a matsayin minista a gwamnatinsa.

Tuni majalisar Dattawa suka tantance shi a matsayin ministan gwamnatin APC, duk da kasancewar shi dan jam'iyyar PDP.

Tsohon Bidiyon Wike Na Cewa Ba Zai Yi Minista Ba Ya Girgiza Intanet

A wani labarin, an gano wani tsohon faifan bidiyo inda tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ke cewa ba zai ta ba zama minista ba.

Wike ya fadi haka ne yayin yakin neman zabe inda ya ce idan har minista daya ake bayarwa a jiha, to ba shi ba ne inda ya ce ya mulki jihar Rivers mai arziki har sau biyu.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya nada shi minista wanda har majalisar Dattawa ta tantance shi a ranar Litinin 31 ga watan Yuli a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel