Ministocin Tinubu: Gbajabiamila Ya Ce Za a Bayyana Ragowar Sunayen Nan Ba Da Jimawa Ba

Ministocin Tinubu: Gbajabiamila Ya Ce Za a Bayyana Ragowar Sunayen Nan Ba Da Jimawa Ba

  • Har yanzu ba a sami sunan ko mutum daya a ministocin Tinubu a jihohi 11 daga cikin 36 da ake da su a Najeriya ba
  • Jerin sunayen ministocin da aka dade ana jira, ya kunshi 'yan jam’iyyar APC mai mulki da kuma wasu masana da suka goyi bayan takarar Shugaba Tinubu.
  • Sai dai Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa kaso na biyu na sunayen zai fito nan ba da jimawa ba, duk da wani rahoto ya nuna cewa rigingimun cikin gida ne ya sa ba a bayyana na jihohin 11 ba

A ranar Alhamis 27 ga watan Yuli ne Shugaba Bola Tinubu ya aikawa Majalisar Dattawan Najeriya jerin sunayen mistocinsa domin tantancewa.

Sai dai jerin sunayen da Tinubu ya aika ya zo ne kasa da sa'o'i 24 da ya kamata Tinubu ya gabatar da shi ga majalisa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, kuma na iya jihohi 25 ne aka bayyana kamar yadda The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

“Ban Taba Haduwa Da Mahaifina Ko Sau 1 Ba”: Ɗan Najeriya Da Ya Shafe Shekaru 29 Yana Nema Danginsa

An bayyana lokacin da za a fadi ragowar ministocin Tinubu
Gbajabiamila ya ce za a sanar da ragowar sunayen ministocin Tinubu nan ba da jimawa ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jihohi 11 da ba a bayyana sunayen ministocinsu ba

Jihohi 11 ne dai har yanzu ba a bayyana sunayen wadanda za a ba mukaman ministoci daga cikinsu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jihohin su ne:

1. Jihar shugaban kasa wato jihar Legas

2. Kano

3. Adamawa

4. Bayelsa

5. Gombe

6. Kebbi

7. Plateau

8. Osun

9. Yobe

10. Zamfara

11. Kogi .

"Kaso na biyi na sunayen ministocin zai fito nan kusa", Femi Gbajabiamila ya yi bayani

Mafi yawan mutanen da sunansu ya fito a jerin ministocin 'ya'yan jam'iyyar APC ne da kuma wasu masana, haka nan ma da Nyesome Wike, jagoran gwamnonin G5 da suka yi wa PDP tawaye.

Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila, ya shaidawa manema labarai a ranar Alhamis cewa sunayen sauran wadanda za a ba ministoci daga jihohi 11 zai fito nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Jerin Ministoci: Faifan Bidiyon Wike Na Alfahari Cewa Ba Zai Yi Minista Ba Ya Jawo Cece-kuce A Intanet

Gbajabiamila ya kara da cewa akwai yiwuwar samar da karin wasu ma'aikatun da suka dace da tsarukan Shugaba Tinubu.

Ana kokarin daidaita ra'ayoyin 'yan siyasar jihohin 11

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta yi, ta bayyana cewa majiyoyi masu karfi sun shaida ma ta cewa ana duba sanin aiki, hidimtawa jam'iyya da sauransu wajen zabar wanda za a bai wa mukamin ministan a jihohin da suka rage.

Rahoton ya kara da cewa rashin samun daidaito a tsakanin 'yan siyasar jihar Kano da na Legas na daga cikin abinda ake ganin ya hana bayyana sunayen ministoci daga jihohin.

Legit.ng ta samu cewa an samu tsaiko wajen bayyana sunan minista daga jihar Gombe saboda wata ba tu da ya janyo tattake wuri.

'Yan Najeriya sun yi martani kan yadda Tinubu ya zabi ministoci

Legit.ng a baya ta yi rahoton kan yadda 'yan Najeriya da dama ke ci gaba da tofa albarkacin bakunansu dangane da jerin sunayen ministocin da Tinubu ya fita.

Kara karanta wannan

Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko

'Yan Najeriya musamman ma dai matasa, sun koka kan yadda jerin ministocin ya kunshi tsofaffin 'yan siyasa ba tare da sanya matashi ko daya ba duk kuwa da irin gudummawar da suka ba da.

Asali: Legit.ng

Online view pixel