Ministocin Tinubu: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Kan Yadda Shugaban Kasa Ya Zabi Ministoci

Ministocin Tinubu: 'Yan Najeriya Sun Yi Martani Kan Yadda Shugaban Kasa Ya Zabi Ministoci

  • Bayan jira da aka dauki makwanni ana yi, a karshe majalisar Dattawa ta sanar da jerin sunayen ministocin Tinubu
  • Sai dai abin bai yi wa mutane da dama dadi ba yayin da suka ci gaba da ganin wasu tsoffin gwamnoni da ‘yan majalisa
  • Sun koka yadda babu matasa a cikin jerin sunayen duk da cewa matasa sun taka rawar gani a lokacin yakin neman zabe

FCT, Abuja – A karshe majalisar Dattawa ta sanar da jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu bayan jiran tsammani na tsawon lokaci.

Majalisar ta sanar da sunayen ministoci 28 ne kadai don tantance su a majalisar Dattawa, Legit.ng ta tattaro.

'Yan Najeriya Sun Yi Martani Kan Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci
Ana Tunanin Korafi Zai Kare Bayan Tinubu Ya Sake Sunayen Ministoci, Ashe Yanzu Aka Fara. Hoto: Nasir El-Rufai, Nyesom Ezenwo Wike.
Asali: Twitter

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya nemo wasu macizai wadanda sanannu ne wajen cin amana kuma ya sakawa wadanda sanannu ne wajen yaudara.

Kara karanta wannan

"Bai Wa Maciji Masauki A Fada Ba Zai Sa Ya Raga Wa Sarki Ba": Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Ministocin Tinubu

Ya bayyana haka a shafinsa na Twitter:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jerin Ministoci; Shugaban kasa ya zabo wasu macizai wadanda tarihi ya nuna maciya amana ne, kuma ya saka wa wasu 'yan bata ruwa domin kowa ya rasa."
"Rarrashin maciji a fada ba ya hana ya sari sarki ."

‘Yan Najeriya sun yi martini akan jerin sunayen ministocin da majalisar Dattawa ta sanar a yau Alhamis 27 ga watan Yuli.

Martanin mutane akan sunayen Tinubu da aka sanar a majalisa

@Mykoladoo:

“Nadin minister ya dawo sakayya ga wadanda suka sha wahala ne kawai, ba wai don nada kwararru da za su kawo ci gaba ba. Jerin tsoffin gwamnoni da ‘yan majalisa, babu abin da matasa shugabannin gobe za su samu.”

@idmann_mit:

“Elrufai ya yi minister shekaru 20, Wike 12 da suka wuce. a jerin ministocin na biyu za ku ga Kwankwaso da ya ki karbar mataimakin shugaban kasa don zama minister. Babu wasu matasa a ciki saboda ba kasa ce a gabansu ba kawai siyasa ce.”

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaba Tinubu

Shehu Sani Ya Yi Martani Kan Sunayen Ministocin Tinubu

A wani labarin, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya yi martani kan sunayen ministocin Shugaba Tinubu.

Shehu Sani ya ce Tinubu ya zabo kuma ya sakawa macizai sanannu maciya amana wanda kowa ya san su.

Sanatan ya gargadi shugaban da ya yi hankali saboda kokarin faranta ran maciji ba zai sa sarki ya tsira ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel