Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Adadin Ragowar Ministocin da Za a Nada

Fadar Shugaban Kasa Ta Fayyace Adadin Ragowar Ministocin da Za a Nada

  • Nan gaba kadan ake sa ran takarar Mai girma Bola Ahmad Tinubu za ta sake shiga majalisar dattawa
  • Gwamnatin tarayya za ta yi wa ma’aikatu garambawul, watakila a bullo da wasu sababbin ma’aikatu fil
  • Femi Gbajabiamila ya ce akwai ragowar sunayen Ministocin da shugaba Tinubu zai aikawa Sanatocin kasar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja – Ba abin mamaki ba ne gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta kirkiro wasu sababbin ma’aikatun tarayya domin Ministocin da za a nada.

A ranar Alhamis, NAN ta rahoto Femi Gbajabiamila yana karin bayani a game da nadin Ministocin gwamnati da aka fara shirin yi a makon nan.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar ya shaida cewa Shugaba Bola Tinubu zai iya fito da wasu sababbin ma’aikatu da Ministocin za su rike.

Ministocin Shugaban Kasa
Bola Tinubu bari gama nada Ministoci ba Hoto: Femi Gbajabiamila
Asali: Facebook

Za a fito da sabon tsari

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana Kan Ma'aikatun da Ministoci 28 Zasu Jagoranta

“Mai girma shugaban kasa ya yi niyyar rarraba ma’aikatu ko ya yi masu garambawul ta yadda yanzu za ku fara jin sunayen wasu ma’aikatu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadannan ma’aikatu ba su cin gashin kan su a baya, sai ayi haka kafin a cigaba da aikin nada su.

- Femi Gbajabiamila

Sai da aka dirje Ministoci tukuna

Daily Trust ta rahoto Gbajabiamila yana cewa an zabo sahun farko na Ministocin nan ne bayan Mai girma shugaban kasa ya yi ta-ka-tsan-tsan.

Hadimin shugaban Najeriyan ya ce nan gaba kadan za a turawa majalisa jeri na biyu wanda zai kunshi karin mutane da za su shiga gwamnati.

Tsakanin 12 ko 13

“Kamar yadda aka karanto wasikarsa a zauren majalisar dattawa, ban san ragowar sunaye nawa su ka rage ba, watalila 12 ko kuwa 13
Za a aikawa majalisar dattawa sunayensu a nan gaba. Game da wadanda aka zabo, sai da shugaban kasa ya tsaya ya bata lokacinsa a kai.

Kara karanta wannan

Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci

- Femi Gbajabiamila

Wasu sun samu, wasu sun rasa

Kun ji labari cewa mutanen Badaru Abubakar, Ezenwo Nyesom Wike, David Umahi Nasir El Rufai su na murnar hango kujerar Ministoci a FEC.

Har tsohon Gwamnan Ebonyi, David Umahi wanda yanzu yana majalisar dattawa, ya samu shiga, amma an yi watsi da wasu tsofaffin Gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel