Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci

Mata 7 Daga Jihohin Katsina, Imo, Abia da Anambra da ke Shirin Zama Ministoci

  • Mata 7 su ka samu shiga cikin sahun farko na Ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fitar a yau
  • Ana kukan cewa mata ba su samun manyan mukaman siyasa da na kujerun gwamnati a Najeriya
  • Zuwa yanzu mata su na da 25% na mukaman Ministocin da ake so a bada a gwamnatin Tinubu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wannan rahoto ya dauko sunayen duka matan da aka aikawa majalisar dattawa sunayensu:

1. Hannatu Musawa

Hannatu Musawa ta rike mataimakiyar mai magana da yawun bakin kwamitin PCC da Bola Tinubu yake neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Wannan lauya tayi gado ne domin mahaifinta shi ne Musa Musawa. Yanzu haka ta na cikin masu ba shugaban kasa shawara, ta na da digiri akalla shida.

Ministoci mata
Matan da za su zama Ministoci Hoto: Barrister Hannatu Musawa, Hon Nkeiruka Onyejeocha, Abdullah Ayofe Olaniyi, Joe Igbokwe
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Jerin Jihohin Da Basu Samu Kujerun Ministoci Ba Zuwa Yanzu a Gwamnatin Shugaba Tinubu

2. Dr. Betta Edu

Dr. Betta Edu ta na cikin shugabannin APC na kasa da za su shigo gwamnati, likitar mai shekara 36 ta yi Kwamishinar lafiya a Jihar Kuros Ribas.

3. Dr. Doris Uzoka-Anite

Doris Uzoka-Anite tsohuwar Kwamishinar tattalin arziki ce a jihar Imo, kwararriyar ma’aikaciyar banki ce wanda tayi fice a mata a ilmin kudi.

4. Hon. Nkeiruka Onyejeocha

Ana sa ran Nkeiruka Onyejeocha za ta koma gwamnati, wannan karo a matsayin Minista bayan rasa kujerar majalisa a bana a dalilin LP a Abia.

5. Stella Okotette

Wata mace da za a tantance a majalisar dattawa domin zama Minista ita ce Stella Okotete. Muhammadu Buhari ya fara nada ta shugabar bankin NEXIM.

6. Uju Kennedy-Ohaneye

Wanda za ta wakilci Anambra a FEC ba kowa ba ce sai Kennedy-Ohaneye. ‘Yar kasuwar ta tsaya takarar shugaban kasa tare da Bola Tinubu a APC.

7. Iman Suleiman Ibrahim

Daga Nasarawa, Bola Tinubu ya bada sunan Iman Sulaiman-Ibrahim wanda ta jagoranci NAPTIP a baya, Iman mai digiri uku ta gama jami’a ta na 19.

Kara karanta wannan

El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Isa Gaban Majalisar Dattawa

Tsofaffin Gwamnoni za su zama Ministoci

Ana da labari Hadiman shugaban kasa kamar Hannatu Musawa, Dele Alake da Olawale Edun za su zama Ministoci idan aka tantance su a majalisa.

Jerin sababbin Ministoci yana dauke da tsofaffin gwamnonin jihohi irinsu Badaru Abubakar, Ezenwo Nyesom Wike, David Umahi da Nasir El Rufai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel