Labari Mai Zafi: Wike, El-Rufai, Badaru Sun Shiga Cikin Ministocin Bola Tinubu 28

Labari Mai Zafi: Wike, El-Rufai, Badaru Sun Shiga Cikin Ministocin Bola Tinubu 28

  • Watakila David Umahi zai bar majalisar dattawa, an bada sunan shi a Ministoci tare da Farfesa Ali Pate
  • Akwai tsofaffin Gwamnoni irinsu Nasir El Rufai, Badaru Abubakar da kuma Ezenwo Nyesom Wike
  • Bello Muhammad Goronyo, Dele Alake, da Lateef Fagbemi SAN sun kama hanyar zama Ministocin tarayya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya na cikin jerin Ministocin Bola Ahmed Tinubu da aka karanto a majalisar dattawa.

Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya na cikin jerin Ministocin Bola Ahmed Tinubu da aka karanto a majalisar dattawa.

A yau Alhamis, fadar shugaban kasa ta aikowa majalisar dattawa sunayen wasu da za a tantance a matsayin Ministocin gwamnatin tarayya.

Ministocin Bola Tinubu
Majalisa ta karbi sunayen Ministocin Bola Tinubu Hoto: @SGFAkume
Asali: Twitter

Tsofaffin Gwamnoni da Hadimai

Jerin yana dauke da tsofaffin gwamnonin jihohi irinsu Badaru Abubakar, Ezenwo Nyesom Wike, David Umahi da kuma Malam Nasir El Rufai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Alhazan Najeriya Sun Makale a Nijar Sakamakon Juyin Mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hadiman shugaban kasa kamar Hannatu Musawa, Dele Alake da Olawale Edun za su zama Ministoci idan aka tantance su a majalisar tarayya.

A jerin akwai Sakataren gwamnatin Katsina, Ahmad Dangiwa wanda ya taba rike FMBN.

UTC da Nnaji sun samu shiga

Farfesoshi sun hada da Abubakar Momoh, Joseph Usev da Muhammad Ali Pate wanda ake hasashen zai zama Ministan harkar kiwon lafiya.

Daga Enugu, an dauko Uche Nnaji wanda ya yi takarar gwamna a APC a zaben 2023.

Wanda aka dauko daga Taraba shi ne tsohon Gwamnan rikon kwarya, Sani Abubakar Danladi, sai Ekerikpe Ekpo zai wakilci Akwa Ibom a FEC.

Daga baya ana sa ran za a aika ragowar sunayen domin kowace jiha ta samu kujera.

Cikakken jerin Ministoci

  1. Abubakar Momoh
  2. Yusuf Maitama Tugga
  3. Ahmad Dangiwa
  4. Hannatu Musawa
  5. Uche Nnaji
  6. Betta Edu
  7. Dr. Diris Anite Uzoka
  8. David Umahi
  9. Ezenwo Nyesom Wike
  10. Muhammed Badaru Abubakar
  11. Nasir El Rufai
  12. Ekerikpe Ekpo
  13. Nkiru Onyejiocha
  14. Olubunmi T. Ojo
  15. Stella Okotete
  16. Uju Kennedy Ohaneye
  17. Bello Muhammad Goronyo
  18. Dele Alake
  19. Lateef Fagbemi
  20. Mohammad Idris
  21. Olawale Edun
  22. Waheed Adebanwo
  23. Emman Suleman Ibrahim
  24. Prof Ali Pate
  25. Prof Joseph Usev
  26. Abubakar Kyari
  27. John Enoh
  28. Sani Abubakar Danladi

Kara karanta wannan

El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Isa Gaban Majalisar Dattawa

Tun da Abdullahi Adamu ya ajiye mukaminsa a APC, ya bar katon gibi a Majalisar NWC, an samu labari Abdullahi Ganduje zai gaje shi.

Abdullahi Ganduje ya na neman kujerar, amma akwai kalubale a gabansa daga Arewa maso tsakiya yankin da tsohon shugaban ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng