Kotu Ta Bayar Da Umarnin Cafke Farfesa Mahmood Yakubu Kan Goge Sakamakon Zabe? Gaskiya Ta Fito

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Cafke Farfesa Mahmood Yakubu Kan Goge Sakamakon Zabe? Gaskiya Ta Fito

  • Kotun sauraron ƙarar zaɓen shugaban ƙasa na ci gaba da sauraron ƙarar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairu
  • A yayin da ake sauraron ƙarar, wasu bayanai sun fito cewa kotun ta bada umarnin cafke shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, bisa goge sakamakon zaɓe
  • An samo cewa babu wata hujja cewa kotun ta bayar da umarnin cafke shugaban hukumar shirya zaɓen ta ƙasa

FCT, Abuja - Watanni bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa na 2023, hukumar INEC, jam'iyyun siyasa da ƴan takarar shugaban ƙasa na ci gaba da fafatawa a kotu kan sakamakon zaɓen.

Amma wani rubutu da aka sanya a Facebook, a cewar Africa Check, wata hukumar tantance labaran ƙarya, ya yi iƙirarin cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, ta bayar da umarnin cafke Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar INEC.

Kara karanta wannan

Zance Ya Ƙare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da Ta Bukaci Tsige Gwamnan PDP

Kotu ba ta bayar da umarnin cafke shugaban INEC ba
Babu wata hujja cewa kotu ta bayar da umarnin cafke Farfesa Mahmood Yakubu Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Babu wata hujja cewa kotu ta bayar da umarnin cafke shugaban INEC kan goge sakamakon zaɓe

Wanda ya yi rubutun ya yi iƙirarin cewa an bayar da umarnin cafke Farfesa Mahmood ne saboda goge sakamakon da ke a cikin na'urar BVAS.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rubutun wanda aka yi a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, na cewa:

"Da ɗumi-ɗumi! Kotu ta bayar da umarnin cafke shugaban INEC bisa goge sakamakon zaɓen da ke a na'urar BVAS."

Bidiyon da aka sanya ya nuna mamallakin shafin Facebook ɗin wanda ya ce ya samu labarin ne daga tashar 'Arise TV news'.

An kalli bidiyon sama da sau 16,000 ya zuwa lokacin da aka gudanar da binciken.

Africa Check ta gano irin wannan labarin a Facebook a nan, nan da nan.

Amma shin kotun ta bayar da umarnin cafke shugaban INEC? Gaskiya ta bayyana.

Kara karanta wannan

Bayan Gana Wa da Tinubu, Shugaban NPC Ya Yi Magana Kan Sabuwar Ranar da Za'a Yi Ƙidaya a Najeriya

Babu hujja cewa an bayar da umarnin cafke shugaban INEC ko tsare shi

Babu wata hujja da za a iya samu a sahihan kafafen watsa labarai wanda zai nuna cewa an cafke Farfesa Mahmood Yakubu bisa umarnin kotun da ke sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Haka kuma babu wasu rahotanni da suka nuna cewa kotun ta bayar da umarnin a cafke shi.

A saboda haka labarin cewa an cafke shi wata ƙarya ce tsagwaronta da masu yaɗa labaran ƙarya suka kitsa.

Batun Gaskiya Kan Haukacewar Dan Shugaban INEC

A baya rahoto ya zo kan gaskiyar batun da aka yi ta yawo da shi cewa yaron shugaban hukumar zaɓe mai zamnta kanta ta ƙasa (INEC) ya haukace a Saudiyya.

Binciken ƙwaƙwaf da aka gudanar ya nuna cewa wannan labarin ƙarya ce tsagwaronta da aka kitsa aka riƙa yaɗa wa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel