Shugaba Tinubu Zai Sanar da Sabuwar Ranar Kidaya a Najeriya

Shugaba Tinubu Zai Sanar da Sabuwar Ranar Kidaya a Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin shugaban hukumar kidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, da tawagarsa a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Nasir Kwarra, ya ce shugaba Tinubu zai sanar da sabon lokacin da za'a yi ƙidaya a Najeriya bayan sun masa bayanin halin da ake ciki
  • Tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ce ta fara shirin ƙidaya amma lokaci ya cimmata ba tare da aiwatar da aikin ba

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanar da sabuwar ranar da za'a gudanar da ƙidayar al'umma da gidaje a Najeriya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Shugaban hukumar kidaya ta ƙasa (NPC), Nasir Kwarra, shi ne ya bayyana haka ga masu ɗauko labaran gidan gwamnati ranar Alhamis a Abuja.

Shugaba Tinubu tare da shugaban hukumar ƙidaya NPC.
Shugaba Tinubu Zai Sanar da Sabuwar Ranar Kidaya a Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Jim kaɗan bayan ya jagoranci tawaga sun yi wa shugaban ƙasa bayanin inda aka kwana a Aso Rock yau Alhamis, Nasir Kwarra ya ce wuƙa da nama na hannun Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Kwanta da Ita, Wani Ɗan Kasuwa Ya Saki Hotuna 50 Na Tsiraicin Wata Mata, Ya Shiga Matsala

Ya ce hukumar NPC ta miƙa rahoto ga shugaban ƙasa kuma tana tsammanin zai yi nazari kansa kuma ya ɗauki mataki da yanke lokacin da za'a gudanar da ƙidaya a faɗin ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yiwuwar mu bukaci ƙarin kuɗi - NPC

Shugaban NPC ya kuma nuna cewa da yuwuwar hukumar ta sake neman ƙarin kuɗaɗe domin a cewarsa tsawon lokacin da aka samu jinkiri, adadin ƙarin kuɗin da za'a buƙata.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban NPC na cewa:

"Mun masa bayani a taƙaice game da shirin da muka yi da kuma hangen mu kuma zan iya cewa shugaban ƙasa ya amince zai tallafa wa NPC ta gudanar da ƙidaya."
"Saboda haka zamu ci gaba da shirye-shirye kuma nan gaba zamu ji daga gare shi, ranar da za'a gudanar da aikin ƙidaya domin mun miƙa masa rahoto wanda zai duba kafin ya dawo gare mu."

Kara karanta wannan

Magana Ta Ƙare: Shugaba Tinubu Ya Ɗora Nauyin Dawo da Zaman Lafiya A Zamfara Kan Mutum 1

"Amma ya ba mu tabbaci da goyon baya kuma mun ji daɗin yadda ya fahimci muhimmancin tattara alkaluman saboda tsare-tsaren ƙasa da ci gaba."

Gwamnatin Kwara Ta Soke Matakin Rage Ranakun Aiki Daga 5 Zuwa 3

A wani rahoton na daban kuma Gwamnatin jihar Kwara ta janye matakin rage wa ma'aikatanta kwanakin zuwa wurin aiki daga kwana 5 zuwa 3.

A sabon umarnin da gwamnatin ta bayar, ta ce kowane ma'aikaci zai koma zuwa wurin aiki tsawon kwanaki 5 a mako kamar yadda aka saba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262