Jam'iyyar PDP Ta Rushe Shugabanninta Na Gudanarwa a Jihohin Ebonyi Da Ekiti

Jam'iyyar PDP Ta Rushe Shugabanninta Na Gudanarwa a Jihohin Ebonyi Da Ekiti

  • Babbar jam’iyyar adawa ta ƙasa wato PDP, ta sanar da rushe duka shugabanninta na gudanarwa da ke jihohin Ebonyi da Ekiti
  • Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC), na jam’iyyar ta PDP ne ya yanke wannan shawara bayan tattaunawa da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki
  • Rushewar dai ta yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta PDP, wanda aka yi wa gyara a shekarar 2017

Abuja - Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) na jam’iyyar PDP, ya rusa shugabannin gudanarwa na jam’iyyar na jihar Ebonyi da na jihar Ekiti ba tare da ɓata lokaci ba.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Mista Debo Ologunagba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna Ya Kara Jiƙa Wa PDP Aiki Kwanaki Kaɗan Bayan Rantsar da Tinubu

Jam'iyyar PDP ta rushe shugabanninta a jihohin Ebony da Ekiti
PDP ta sanar da rusa shugabanninta na gudanarwa a jihohin Ebonyi da Ekiti. Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Kwamitin ayyuka na PDP ne ya yanke hukuncin

Ologunagba ya ce kwamitin ayyuka na jam'iyyar ta PDP ne ya amince da rusa shugabannin gudanarwa na jihohin biyu bayan tattaunawa da kuma tuntuba da sauran 'yan jam'iyya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce matakin na kwamitin aikace-aikace, ya kasance ne a ƙarƙashin sashe na 29 (2) (b) da 31 (2) na kundin tsarin mulkin PDP (kamar yadda aka gyara a shekarar 2017).

PDP ta rushe shugabanninta na jihar Ebonyi da Ekiti
Jam'iyyar PDP ta sanar da rushe shugabanninta a jihohin Ekiti da Ebonyi. Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

An yi kira ga 'yan PDP a jihar su zamto masu haɗin kai

An yi kira ga 'yan jam'iyyar PDP a waɗannan jihohi guda biyu da su ci gaba da zama cikin haɗin kai a tsakaninsu gami da mayar da hankali kan abubuwan da suka dace.

A cewar Ologunagba:

"PDP na kira ga dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan 'yan jam'iyyarmu a jihohin Ebonyi da Ekiti da su kasance cikin haɗin kai tare da mai da hankali kan abinda da ke gabansu,".

Kara karanta wannan

Muna Da Bidiyon Yahaya Bello Yana Ikirarin Cewa Shi Gwanin Iya Harbi Ne, Cewar Dan Takarar SDP

Sanarwar dakatarwar ta fito ne da yammacin ranar Laraba, a shafin Tuwita na jam'iyyar ta PDP.

An ba Tinubu shawara kan yadda zai biyawa Najeriya bashi

A wani labarin na daban, mun kawo muku yadda wani fitaccen ɗan kasuwa, Jimoh Ibrahim, ya bai wa sabon shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan yadda zai biyawa Najeriya bashin da ake bin ta.

A hirarsa da gidan talabijin na Channels, Jimoh ya bayyana matakan da Tinubu ya kamata ya bi wajen biyawa Najeriya duka basussukan da ake bin ta a cikin wata uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel