Muna Da Bidiyon Yahaya Bello Yana Ikirarin Cewa Shi Gwanin Iya Harbi Ne, Cewar Dan Takarar SDP

Muna Da Bidiyon Yahaya Bello Yana Ikirarin Cewa Shi Gwanin Iya Harbi Ne, Cewar Dan Takarar SDP

  • Mai magana da yawun ɗan takarar gwamna na jam'iyyar SDP a jihar Kogi, Farouq Adejoh ya zargi Yahaya Bello da tada hankulan jama'a
  • Ya ce suna da bidiyon inda Yahaya Bello ya yi iƙirarin cewa shi gwani ne a wajen iya harba bindiga, fiye da duk wani mutum ma
  • Ya kuma ce tarihin Gwamna Yahaya Bello cike yake da rikice-rikice da kuma tashin hankali, inda ya ce da haka ne ma ya ƙaƙaba ɗan takarar da ya tsaida

Lokoja - Farouq Adejoh, mai magana da yawun ɗan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar Kogi, Muritala Yakubu Ajaka, ya ce jam’iyyar na da bidiyon gwamna Yahaya Bello yana gadarar cewa shi gwanin harbi ne.

Adejoh ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Tona Asirin Wasu Gwamnoni da Suka Rika Ma'amala da Yan Ta'adda a Jihohinsu

Ya yi tsokaci ne kan rikicin da aka samu tsakanin ayarin motocin gwamnan da na ɗan takarar gwamna na jam’iyyar SDP a jihar.

Yahaya Bello ya yi burgar cewa ya iya harbi
An zargi Yahaya Bello da yin barazanar iya harba bindiga. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A ranar Asabar ne dai tawagar yaƙin neman zaɓen Ajaka da ayarin Gwamna Yahaya Bello suka yi arangama, wanda ya kai ga jikkata wasu mutane daga ɓangarorin biyu, sai dai ba a samu asarar rai ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adejoh ya zargi Yahaya da ƙaƙaba ɗan takara ta ƙarfi da yaji

Da yake ƙarin haske game da lamarin, Adejoh ya zargi Yahaya Bello da yin amfani da ƙarfi wajen ƙaƙaba dan takarar da yake so a zaɓe mai zuwa.

Ya ƙara da cewa Bello ya hau mulki ne dama ta hanyar gadar kujerar da ya yi, yanzu kuma ya yi amfani da ƙarfi wajen sanya ɗan takararsa a zaɓen fidda gwani da ya gabata.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: INEC Ta Saki Jerin Sunayen 'Yan Takarar Gwamna a Jihohin Kogi, Bayelsa Da Imo

Ya kuma bayyana cewa tarihin Gwamna Yahaya Bello cike yake da rikice-rikice da nuna ƙarfi kan abin da yake nema.

An ƙona gidan wani mutumi saboda ƙin goyon bayan ɗan takara

Ya ce akwai wani shahararren mutum da gwamnan ya sa aka ƙonawa gida saboda ya ƙi goyon bayan Alhaji Mudi, duk kuwa da kasancewarsa ɗan jam'iyyar APC ne shima, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A kalamansa:

“Ku dubi Yahaya Bello cikin girmamawa. Shi ne gwamnan jiharmu, amma ku dubi tarihinsa. Yana da tarihin tada hankula a kansa. An ƙona gidan wani Kabiru. Ya kasance ɗan APC ne, amma ya yanke shawarar ƙin goyon bayan Alhaji Mudi. Shahararren mutum ne a Kogi ta Gabas.”
“Idan za ku iya tunawa a lokacin zaben 2019, an ƙona hedikwatar yaƙin neman zaɓen Nrasha. An kuma ƙona wata mata Solumi. Hujjojin hakan suna nan a ajiye. Muna da bidiyon Yahya Bello yana gadarar cewa ya fi kowane mutum iya harba bindiga.”

Kara karanta wannan

Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Bayyana Yadda Ya Sha Da Kyar a Hannun 'Yan Daba a Kotu, Ya Nemi Wata Muhimmiyar Alfarma

Tinubu zai gana da gwamnoni, sanatoci da masu ruwa da tsaki

A wani labarin da Legit.ng ta kawo muku a baya, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi ganawa ta musamman da manyan jam'iyyar APC da suka haɗa da Gwamnoni, Sanatoci da 'yan kwamitin ayyuka.

Tinubu zai dai gana da su ne gabanin zaɓen majalisa ta 10 da ke ta ƙara gabatowa, wanda jam'iyyar ta APC ta tsaida waɗanda take so su jagoranci tagwayen majalisun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel