Fitaccen Attajiri Ya Ba Najeriya Shawarar Yadda Za Ta Biya Bashin N77tr a Kwana 90

Fitaccen Attajiri Ya Ba Najeriya Shawarar Yadda Za Ta Biya Bashin N77tr a Kwana 90

  • Jimoh Ibrahim ya na ganin Najeriya za ta iya biyan bashin da ake bin ta a cikin watanni uku
  • Zababben Sanatan ya ba Bola Tinubu lakanin lakanin yadda zai huta da tulin bashin da ya gada
  • A majalisa ta goma, Dr. Ibrahim ne zai wakilci yankin Kudancin jihar Ondo a Majalisar Dattawa

Abuja - Zababben Sanatan yankin Kudancin jihar Ondo, Jimoh Ibrahim, ya kawo shawarar yadda gwamnatin tarayya za ta biya bashin da yake kan ta.

Da aka yi hira da shi a gidan talabijin Channels, Dr. Jimoh Ibrahim ya ce hukumomin Najeriya su nemi bankunan EXIMS, su sake karbo wasu karin bashin.

Attajirin yake cewa a nemi irin wadannan bankuna biyar, sai a karbo bashin da ya nunka wanda yake wuyan gwamnatin Najeriya a yanzu sau biyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Ƙara Albashi, Ya Rage Ranakun Zuwa Aiki Saboda Tashin Kudin Man Fetur

Bola Tinubu
Bola Tinubu wajen wani taro da 'yan kasuwa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Biyan bashi da bashi

Sanatan mai-jiran gado ya ce sai ayi amfani da kudin da aka aro domin biyan tsofaffin bashin da yake kan Najeriya, kuma a samu ragowar canji.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Zan iya baku dabarar da za ta sa mu biya bashinmu a cikin kwanaki 90. Abin da kurum za ayi shi ne a kira bankunan EXIM, har da na kasar Sin.
A karbo aron abin da ya nunka kudin da ake bin mu bashi sau biyar, sai a biya rarar kudin da ake bin mu. Daga nan za a samu rarar kudi sun rage.
Sai a fito da tsarin biyan bashi na shekara 40, daga nan za a samu wa’adin shekaru 10 na biyan bashi, shikenan an fita daga cikin kangin bashi.”

- Jimoh Ibrahim

A hirar da aka yi da shi, ‘dan kasuwan da ya koma siyasa ya tabo batun rashin tsaro musamman ‘Yan Boko Haram da suka dauki shekaru su na ta’adi.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Yakin Boko Haram

Jimoh ya na ganin akwai siyasa a game da lamarin ta’addacin Boko Haram, ya ba Bola Ahmed Tinubu shawarar ya umarci sojoji su bar filin daga.

Vanguard ta ce zababben ‘dan majalisar ya koka game da lamarin, ya ce sai sojoji sun canji tsari.

Attajirin ya ce an kashe Dala tiriliyan 1.2 wajen tunkarar ta’addanci, amma har yau lamarin bai kare ba, a cewarsa ya kamata a nemi wani salon yakin.

Cire tallafin man fetur

An ji labari Gwamnatin Bola Tinubu za ta kara albashin ma’aikata kuma za a kawowa talaka sa’ida domin a samu saukin rayuwa saboda tashin fetur.

Baya ga tsare-tsaren da NEC za ta kawo, 'yan kasuwa sun yi alkawarin kashe kusan Naira Biliyan 10 a wajen raba manyan motoci masu daukar fasinjoji 50.

Asali: Legit.ng

Online view pixel